Sabuwar dokar hakar man fetur da gas a Tanzaniya
July 6, 2015Talla
A Tanzaniya majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wata sabuwar dokar tsarin aikin hakar man fetur dama gas na girki a ƙasar.A ƙarƙashin sabuwar dokar dai wacce ake jira a nan gaba shugaban ƙasar ya sanya mata hannu gwamnati ce za ta mallaki kishi 60 zuwa 80 daga cikin ɗari na arzikin gas na girki da ƙasar ke fitar wa daga ƙarƙashin ƙasa da kuma kishi 85 daga cikin dari a kan wanda za ta haƙo a cikin ruwa.
Haka zalika dokar ta tanadi cewar idan ƙasar ta samo man fetur wanda ake nan ana gudanar da bincike a kai to kuwa gwamnati ce za ta mallaki kishi 50 zuwa kashi 70 daga cikin ɗari na wannan arziki.