Nijar: Kaddamar da yaki da Maleriya
October 18, 2018Kungiyar Tarayyar Afirka AU ce dai ta bullo da tsarin tare da bukatar daukacin kasashen nahiyar su rungume shi. Kafin nan da shekara ta 2030 za a yi wa yara jarirai daga haihuwarsu rigakafin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauron. A yanzu dai zazzabin na cizon sauro na zaman guda daga cikin cututtuka biyar da suka fi hallaka yara kanana 'yan kasa da shekaru biyar da ma janyo mutuwar mata masu juna biyu kafin da kuma yayin haihuwa. Baya ga wannan ma, kiyasi ya nunar da cewa cutar zazzabin cizon sauron wato maleriya na zaman cuta ta kan gaba da ke haddasa mutuwa fiye da kima a Afirkan.
Cibiyar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta Jamhuriyar ta Nijar da ke karkashin ofishin ministan kiwon lafiya ce dai ta shirya wannan taro. Wakilai da dama daga kasashen Afirka da ma wakili daga kungiyar Tarayyar Afirkan suka halarci taron kaddamar da sabon tsarin yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro wato maleriya, inda daga bisanin dukkanin kasashen nahiyar Afirkan za su fara gudanar da tsarin a kasashensu.