Sabon ministan harkokin wajen Jamus, Frank -Walter Steinmeier.
October 13, 2005Kafin bayyana sunansa dai, babu wanda ya san Frank Walter Steinmeier a fagen siyasar Jamus. To nan ba da dadewa ba kuwa, shi ne zai zamo ministan harkokin wajen Jamus, a sabuwar gwamnatin da za a kafa karkashin jagorancin Angela Merkel. Da can dai, Steinmeier na daya daga cikin `yan hannun daman Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin tarayya mai barin gado. Ya taka rawar gani wajen bai wa shugaban shawara kan batutuwan siyasa masu jirkitaswa. Kai saboda kwarewarsa a harkokin siyasa, jam’iyyun adawa ma sun sha yabonsa. Kamar yadda Michael Glos, shugaban reshen jam’iyyar CSU a majalisar dokoki ta Bundestag ya bayyanar:-
„A gani na dai, mutum ne mai kwazzo, wanda kuma zai iya rike ko wane mukami.“
Shi dai, Steinmeier, ministan harkokin wajen Jamus mai jiran gado, mai shekaru 49 ne da haihuwa, kuma karatun shari’a ya yi, yana da digirin koli, wato PhD a wannan fannin. Duk abokan huldarsa dai sun ce, mutum ne mai fara’a, wanda kuma ya san inda ya nufa.
Daga shekarar 1996 zuwa 1998, shi ne shugaban ofishin Gerhard Schröder, yayin da yake rike da mukamin gwamnan jihar Niedersachsen.
Bayan zaben da aka yi a shekarar 1998, inda Gerhard Schröder ya zamo shugaban gwamnatin tarayya, Steimeier ya bi shugaban zuwa Berlin, inda a nan ma ya zamo jagoran ofishin shugaban gwamnatin. A wannan mukamin kuwa, kullum bas a rabuwa da shugaba Schröder. Ya sha dai bai wa shugaban shawarwari kan muhimman batutuwan da suka shafi manufofin siyasar harkokin wajen Jamus. A duk wasu tarukan da shugaban zai kira kan siyasar harkokin waje, alal misali a kamar a lokacin da aka kai harin kunan bakin waken nan na ran 11 ga watan Satumba a Amirka, Frank Walter Steinmeier na cikin wadanda ake tuntuba. Kazalika kuma ya taka rawar gani wajen tsara manufofin Jamus game da batun yakin Iraqi.
Frank-Walter Steinmeier, yana da aure, kuma yana da `ya mace guda daya tak.