1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon matakin tsagaita wuta a Yemen

Gazali Abdu TasawaJuly 25, 2015

Matakin tsagaita wutar na kwanaki biyar zai soma aiki daga karfe 12 na dare na ranar Litanin mai zuwa domin kai magunguna da abinci ga al'umma.

https://p.dw.com/p/1G4ic
Jemen Taiz Humanitäre Hilfe
Hoto: Reuters/F. Al Nassar

Kawancen kasashen Larabawa da kasar Saudiyya ke jagoranta a cikin yakin kasar Yemen, ya bada sanarwar tsagaita wuta na wa'adin kwanaki biyar daga karfe 12 na dare na ranar Litanin mai zuwa. Kawancen wanda ke da kwarin gwiwar nasarorin da ya ke samu a 'yan kwanakin bayan nan a kan abokanan gabarsa na 'yan tawayen Houtsi ya ce ya dauki matakin tsagaita wutar ne domin baiwa kungiyoyin agaji damar isar da kayayyakin masarufi da al'ummar yakin wadanda yakin ya rutsa da suke bukata.

Sai dai kawancan sojojin kasashen da Saudiyyar ke jagoranta a cikin wannan yaki na kasar Yemen ya ce ya na da 'yancin mayar da martani a cikin wadannan kwanaki na tsagaita wutar idan har abokanin gabarsu na Houthis suka ci gaba da gudanar da ayyukan sojinsu.