1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake a Istanbul

Salissou BoukariMarch 19, 2016

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bam a tsakiyar birnin Istanbul na kasar Turkiya inda ya hallaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1IGKJ
Türkei Anschlag in Istanbul
Tsakiyar birnin Istanbul na kasar Turkiya inda aka Kai hariHoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

Harin kunar bakin wake na birnin Istanbul da ya afku da safiyar wannan Asabar din an kai shi ne a wani babban titi da ake kira Istiklal da masu tafiya a kafa ke bi, inda ake da tarin manyan shagunan sayar da kayayyaki. Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla biyar tare da jikkata wasu mutane sama da 20 a cewar gwamnan birnin na istanbul. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da birnin na Istanbul ke fuskantar iri wannan hari na 'yan kunar bakin wake. Koda a ranar 12 ga watan Janairun da ya gabata ma dai wani dan kunar bakin waken ya tashi bam din da ke jikinsa a wurin da masu yawon buda ido 'yan kasashen waje suka fi halarta, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 10 akasarinsu 'yan kasar Jamus.