Sabon Gangamin adawa a Togo
December 3, 2017Talla
Mutumin da ya mulki Togo na tsawon shekaru 15 Gnassinbe dai, ya yi alkawarin tattaunawa da kungiyoyin 'yan adawa a watan Nuwamban da ya gabata, tattaunawar da har yanzu bai kaddamar ba makonni bayan alkawarin.
Masu shiga tsakani na yankin yammacin Afirka da suka hadar da shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa na Gini Alpha Conde, sun sha kokarin ganin an bude wannan tattaunawar ta da ci tura kawo yanzu.
Tun a shekara ta 2005 ne da Gnassingbe ya dare kujerar shugabancin kasar ta Togo biyo bayan mutuwar mahaifinsa Janar Gnassingbe Eyadema, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 38.