1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon fasalin NNPC da zuba hannun jari

Ubale Musa AMA(ATB)
July 19, 2022

Babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC na shirin gogayya da takwarorinsa na fadin duniya ta fuskar makashi, bayan ya shafe shekaru 45 yana hada.hadar man fetur.

https://p.dw.com/p/4ENG1
Nigeria I Matatar mai
Najeriya I Matatar man fetur I Matatar inganta dangogin man feturHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa tarihi inda ya yi nasarar kafa kamfanin mai mallakar gwamnati shekaru 45 da suka wuce. Ya rusa kamfanin bayan da ya hau kan mulki, sannan kuma a yanzu Shugaba Buhari ya sake kaddamar wani sabon kamfani NNPC.

Duk da kasancewarsa mafi girma a nahiyar Africa, kamfanin mai na NNPC ya shafe shekarun yana zama matattarar alfarmar jiga-jigan da ke mulki da 'yan cuwa-cuwa dama jagororin siyasa, kafin kafa dokar masana'antar mai a bara da ake ganin ta samar wa kamfanin 'yanci da dora shi kan turbar kasuwa mai cike da doka da tsari.

Karin Bayani: Hukumar gudanarwa ga NNPC a Najeriya

A bikin da ya samu halartar daukaci masu ruwa da tsaki a harkokin Najeriya, kamfanin NNPC ya diga dan ba na goga kafada a kamfanonin duniya na hada-hadar man fetur da iskar gas da ma makamashin man fetur a cewar Mele Kolo Kyari jagoran kamfanin.

Nigeria I Gidan mai
Najeriya I Gidan sayar da man fetur mallakar kamfanin NNPCHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Kamfanin NNPC na zaman daya tilo da ya dauki lokaci yana hannun masu mulki, kuma ya kare da zama kurar baya a tsakanin yan uwansa kamfanoni da ke aikin hada-hadar mai. "Ana ganin sabon tsarin zai bude wani sabon babi da ke shirin daukar nauyin makamashi a nahiyar Afirka don ingantashi ga manyan kasashen yammacin duniya." In ji Dr Umar Farouk Ibrahim sakataren kungiyar kasashen Africa masu arzikin man fetur.

Karin Bayani: Najeriya ta ci ribar man fetur a karon farko cikin shekaru 44

Komai a ke ciki a tsakanin kasashen Turai da ke dakon samun dama dagha kasashe irinsu Najeriya a fafutikar neman makamashi don maye gurbin Rasha. A shekarar bara kadai dai  kamfanin NNPC ya samar da ribar da ta kai Naira Miliyan dubu 240 a baitulmalin kasar a wani abun dake zaman matakin farko ga kamafanin bayan an shafe shekaru da dama.