Harin tsageru a yankin Niger Delta
May 20, 2016Wasu shedun gani da ido da wadanda lamarin ya faru a wurin da suke a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya sun bayyana cewa a ranar Alhamis 19 ga wannan wata na Mayu an kai farmaki a yankin nasu. An kai farmakin ne a yankin Warri a bututun da ke rarraba mai zuwa wasu sassa daban-daban na kasar. Najeriya dai na kara ganin ayyukan na 'yan ta'adda masu fasa bututun mai a yankin na Niger Delta a 'yan makwannin nan, sakamakon aiyukan tsagerun da suka bayyana sunansu da Niger Delta Avengers.
Eric Omare da ke magana da yawun matasa 'yan kabilar Ijaw ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Ogbe Ijoh a kusa da birnin Warri. Shi dai Dadiowei da ke zaune a wannan yanki ya ji kara mai karfin gaske a kan bututun mai mallakar kamfanin NNPC a kauyen nasu cikin daren da ya gabata, abin da ya sanya al'umma a wannan kauye suka shiga rudani. Babu dai wani karin bayani da aka samu daga bangaren mai magana da yawun kamfanin na NNPC a Najeriya.