Ruruwar wutar rikici a gabashin Ukraine
November 10, 2014Frank-Walter Steinmeier y ayi kira ga bengarorin da suka hada, da na gwamnatin Ukraine da 'yan awaren gabashin kasar, da ma kasar Rasha, da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ta ran biyar ga watan Satumba a birnin Minsk na Belarus.
Shugaban Diflomasiyar kasar ta Jamus ya yi wadannan kalamai ne yayin wata ziyara da ya kai a Kazakhstan, inda ya ce jarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, na ci gaba da fuskantar kalubane tun farkon ta. Daga na su bengare wakilan kungiyar tsaro da halin kan Turai ta OSCE, masu saka ido kan batun tsagaita wuta a gabashin kasar ta Ukraine, sun nuna damuwarsu kan yadda su ke ganin tankokin yaki masu yawan gaske a yankunan dake hannun 'yan awaren.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo