1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AES: Kafa rundunar tsaron hadin gwiwa

Gazali Abdou Tasawa LMJ
March 7, 2024

Kasashen Sahel na kungiyar AES da suka hadar da Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, sun cimma matsayar kafa rundunar hadin gwiwa da za ta yaki da ta'addanci a kasashensu.

https://p.dw.com/p/4dH3K
Mali | Assimi Goïta | Nijar | Abdourahamane Tiani | Burkina Faso | Ibrahim Traoré
Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Shugabannin hafsoshin sojojin kasashen na Nijar da Mali da Burkina Faso da suka kira kansu da AES ne, suka cimma wannan matsaya a karshen wani taro da suka gudanar a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar. Sun dai yi bitar yanayin tsaro da yankin yake ciki da kuma nazarin hanyoyin tunkarar matsalar ta'addancin, wacce ke ci gaba da lakume rayukan dubban jama'a a yankin. Tun tashin farko dai kasashen uku wadanda daga bisani suka koma a karkashin ikon mulkin soja sun kafa sabon kawancen AES ne da nufin yaki da matsalar ta ta'addancin, to sai dai watanni bayan kafa kungiyar matsalar ta'addancin ta ci gaba da kasancewa tamkar ana magani kai na kaba. 'Yan ta'addan sun ci gaba da salwantar da rayukan al'umma, ba tare da kowace daga cikin kasashen uku ta iya shawo kann matsalar ba.

ECOWAS | CEDEAO | Jamhuriyar Nijar | Mali | Burkina Faso | Sahel | AES
Shugabannin mulkin sojan kasashen uku sun ayyana fita daga ECOWAS ko CEDEAOHoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Domin yi wa tubkar hanci ne a yanzu kasashen uku suka dauki matakin yi wa matsalar taron dangi, ta hanyar kafa rundunar hadin gwiwa wacce za ta yi yaki da ta'addancin gadan-gadan. Tuni dai wasu 'yan Nijar suka fara nuna goyon bayansu ga shirin kafa rundunar hadin gwiwar, domin yaki da ta'addanci a kasashen na AES. To sai dai Malam Mahamadou Abdoulkader mai adawa da mulkin soja a Nijar na ganin, kafa wannan rundunar hadin gwiwa wani mataki ne na son yi wa Nijar din wayo. Yanzu dai al'ummomin kasashen na AES sun zura ido su ga matakan da shugabannin kasashen uku wadanda da ma ke da raunin tattalin arziki za su dauka wajen samar da kudin daukar nauyin rundunar, ta yadda ba za ta haifi bakwaini ba ko kuma yin raggon kaya tun ba aje ko ina ba kamar yadda ta kasance wa marigayiya rundunar G5 Sahel.