1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya za su bar Kwango

Abdoulaye Mamane Amadou
November 22, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta cimma matsaya da gwamnain Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango kan batun janye dakarunta na Monusco daga kasar a cikin hanzari.

https://p.dw.com/p/4ZKfS
DR Kongo MONUSCO
Hoto: MONUSCO/Xinhua/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da matakin a wata sanarwar da ta fitar a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, sai dai a cikin sanarwar ba a yi wani karin haske kan jadawalin ficewar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

Tun a shekarar 1999 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta girke rundunar tsaro da kwanciyar hankali ta Monusco a Kwangon, wacce ke kumshe da dakaru dubu 14 galibi a yankin gabashin kasar.

Yawaitar hare-haren 'yan bundiga da kazancewar al'amurra, sun sa gwamnatin Kwangon ta bukaci da a janye dakurun cikin hanzari a gabanin sake wa rundunar sabon wa'adi.