Rukunin farko na motocin kayan agaji ya isa Gaza
October 21, 2023Talla
Wannan dai shi ne karon farkon da aka isar da kayan agaji zuwa Gaza tun bayan fara rikici tsakanin Isra'ila da kuma kungiyar Hamas fiye da makwanni biyu da suka gabata.
Mashigin iyakar Rafa na kasance hanya daya tilo zuwa Gaza da ba ya karkashin ikon Isra'ila, inda aka amince da shigar da agaji daga Masar bayan da Amirka da ke dasawa da ita ta bukaci yin hakan.
Karin bayani: Za a fara shigar da kayan agaji Gaza
Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya yi gargadin cewa, kada rukunin farko na kayan agajin ya kasance na karshe.
Dama dai an dauki tsawon kwanaki, jiragen sama da kuma motocin dakon kaya na kai kayan agaji zuwa iyakar ta Rafa, sai dai ba su sami damar isar da su zuwa Gaza ba.