Rudanin siyasa a Cote d'Ivoire
July 9, 2020Rasuwar firaministan Cote d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ta ta jefa siyasar kasar cikin halin rashin tabbas yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe cikin watanni uku masu zuwa.
Kafin rasuwarsa Amadou Coulibaly shi ne wanda Shugaban kasar ta Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya tsayar domin yi wa jam'iyyar RHDP mai mulki takarar shugabancin kasa a zaben mai zuwa.
A halin da ake ciki dai hankula sun karkata ga wanda Jam'iyyar za ta zaba domin maye gurbin Amadou Coulibaly a matsayin dan takara a zaben da ake yi wa kallo a matsayin zakaran gwajin dafi na dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mai arzikin Cocoa.
Firaminista Amadou Gon Coulibaly ya rasu a jiya Laraba yana da shekaru 61 bayan wata 'yar rashin lafiya yayin taron majalisar ministoci.