Takaddamar kwaso mutane daga Sudan
May 2, 2023A Najeriya jinkirin da ake samu na kwaso ‘yan kasar da yakin da ake a Sudan ya rutsa da su fiye da mako guda ya haifar da tambayoyi a kan me ke faruwa ne, musamman batun yayar motocin safa-safa da suke kwaso mutane zuwa kan iyakokin Sudan din da ake nuna ‘yar yatsa a kan ma'aikatar kai daukin gaggawa ta kasar.
Jinkirin da mahukuntan Najeriya suka danganta da hana bada iznin daga bangaren kasar Masar ga ‘yan Najeriyar suk tsallaka ta kan iyakar Aswan don a kwaso su. Masar ta hana baiwa ‘yan Najeriyar iznin tsalkawa ta kasarta. Tuni ofishin jakadancin Najeriya da ke Sudan ya bayyana cewa babu hannunsu a hayar motocin safa-safa da Najeriyar ta kebe dala milyan 1.2 da ake samun cikas.
A yayin da mahukuntan Najeriyar suka bayyana cewa Masar din ta bada ka'idoji na barin ‘yan Najeriya su tsallaka kasarta da suka hada da samar da jirgin da zai dauko su zuwa Najeriya da tabbatar da cewar da sun shiga kasar kai tsaye za su wuce tashar jirgi don kwaso su zuwa Najeriya. Duk da wannan har yanzu babu wanda ya samu shiga kasar.
Akwai dai ‘yan Najeriyar da bisa kashin kansu suka dauki nauyin tafiyarsu tun daga Khartoum inda suka bi ta kan iyakar kasar Habasha, wasu daga cikinsu tuni sun iso Najeriya.
A yayin da ake ci gaba da jiran fara isowar ‘yan Najeriyar da ke a Sudan ko dai ta masar ko kuma ta Jedda na kasar Saudiyya, iyaye da ‘yan uwan 'yan Najeriya na cike da kosawa na ganin an kwaso su zuwa Najeriyar.