Ruɗani dangane da babban taron ƙasa na jam'iyyar PDP
August 29, 2013Kama daga Legacy House da ke zaman hedikwatar haɗa taro na ƙasa na jam'iyyar PDP, ya zuwa Eagles Square da ke zaman zauren taron dai, al'amura sun fara daukar harami. Ga jam'iyyar da a karo na biyu cikin ƙasa da tsawon shekara guda ke sake ƙoƙarin zaɓen shugabannin da za su ja ragamar harkokinta har na tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.
Rikici na cikin gida game da gwagwarmayar neman ikon fada ajin jam'iyyar dai, sun yi ruwa sun yi tsaki wajen mamaye fatan PDP na ci gaba, a ƙoƙarinta na zama ɗaya tilo ta kan gaba a fagen siyasar ƙasar ta Najeriya.
Ana dai kallon sabon zaɓen a matsayin wani ƙokarin cika umarni na hukumar zaɓen da ta zauna ta faɗawa masu gidan na Wadata cewar fa, hanyar zaɓukan shugabanninsu a matakai daban-daban ba sa bisa ka'ida.
Abun kuma da ya kai ga tilasta jam'iyyar yin ƙasa daga dokin girma, tare da tsara gudanar da shirin da ya fuskanci jerin kalubale a kotuna daban daban.
Ya zuwa yanzu a cewar Malam Ilyasu Dhacko da ke zaman ɗaya daga cikin 'yan kwaimitin yada labaran taron na ƙasa dai, komai ya kammala kuma lokaci kawai suke jira.
Fargabar tashin hankali a lokacin taron PDP
Jira na lokaci ko kuma kokarin bai wa maras da kunya dai, ana shirin gudanar da sabon taron ne a cikin ruɗani na tsaro sakamakon bayanan jami'an tsaron ƙasar da ke cewar sun gano wani shiri na tada hankula da nufin hana taron.
Majiyoyin tsaron ƙasar ta Najeriya dai sunce wata ƙungiyar da ta kira kanta PDP Justice and Peace Movement dake fafutukar tabbatar da komawar mulki ya zuwa sashen na arewa, ta shirya gangami a zauren taron, da nufin tilastawa PDP amincewa bisa yarjejeniyar komawar mulki ya zuwa sashen.
To sai dai kuma a hirar da na yi da shi ta wayar tarho mataimakin shugaban jam'iyyar na sashen arewa maso yammacin kasar, Senator Ibrahim Kazaure, ya ce zargin jami'an tsaron kasar shifcin gizo ne kawai.
Ko bayan rikicin gwagwarmayar kujerar mukin dai, PDP na shirin zuwa zaɓen a cikin wani ruɗanin da ya kama hanyar waje road da manyan jiga-jigan jam'iyyar .
Makomar shugabannin PDP na yanzu
Ya zuwa yanzu dai 'yan takarar biyu ne ke ikirarin wakiltar jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar Anambaran da a ka tsara a watan Nuwamba mai zuwa, abun kuma dake kara fitowa fii da irin rabuwar kan dake karin tasiri a cikin jam'iyyar.
An dai kira karɓar na goro kusan Naira Miliyan dubu ɗaya a cikin shirin da ya kalli taruka guda biyu a cikin makon jiya a garin a kwai , kuma a fadar Shehu Musa Gabam, da ke zaman jigon PDP ya tilasta ɗaukar matakin gaggawa da nufin ceto jam'iyyar daga rushewa.
An dai share tsawon daren wannan Larabar ana gudanar da tarukan man'yan masu fada ajin jam'iyyar, da nufin ɓullowa batun na Anambara dama ragowar rigingimun da ke zaman tarnaƙi ga ƙoƙarin jam'iyyar na ci gaba.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh