Rikicin zabe ya bar baya da kura
January 8, 2021Talla
Hukumar Tallafa wa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda suka bar kasar Afirka ta Tsakiya zuwa kasashe makwafta na neman agajin gaggawa na ruwa da abinci da matsugunni da kuma kiwon lafiya. Hukumar zaben kasar dai ta bai wa shugaba mai ci Faustin Touadera a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar Litinin sai dai 'yan adawar kasar sun yi kira da a soke zaben saboda zargin tafka kura-kurai.Jamhuriyar Afirka ta tsakiya dai na daga ciki kasashen da ke fama da talauci a duniya kuma ta fuskanci jerin juiyn mulki da yake-yake tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.