Rikicin sakamakon zabe a Togo ya lafa
May 13, 2005Bisa dukkan alamu an fara gano bakin zaren warware rikicin da kasar Togo ta fada,tun bayan zaben shugaban kasa a watan daya gabata.
Jammiyar hadin gwiwa ta yan adawa a Togo ta bayyana cewa tana laakari da hadewa a gwamnatin hadin kan kasa da aka nada a karkashin jagorancin Faure Gnassingbe,dan tsohon shugaban kasa marigayi kuma mutumin daya samu nasara da kuriu mafi rinjaye a zaben daya gudana ranar 24 ga watan Afrilu a wannan kasa.
Sakamakon zaben shugaban kasa a Togon dai ya kawo tashe tashen hankula daga bangaren magoya bayan jammiiyyun adawa ,wadanda sukace an tabka magudi,rikicin daya jagoranci ficewan sama da mutane dubu 23 zuwa kasashe dake makwabtaka da Togo,ayayinda da dama suka rasa rayukansu kana wasu suka jikkata.
Shugaban yan adawa Yawovi Agboyibo ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa suna nazari a tsakanin wakilansu,kana zasu bada sanarwar matsayi da suka dauka wa gwamnatin kasar ranar talata mai gabatowa.
Zababben Shugaba Gnassimbe dai yayi tayin kafa gwamnatin hadin kan kasa,amma shugabannin jammiyun adawan sunyi watsi da wannan tayin kai tsaye a baya,inda suka nemi a sake kidayan kuriu da aka kada,domin bazasu iya aiki a karkashin shugaban daya ci zabe da magudi ba.
Shugabannin kasashen Afrika,a kokarinsu na kare sake barkewan rikici a nahiyar,a farkon wannan wata ne suka gana da bangarorin dake wannan rikici na Togo,inda suka bukace su dasu koma teburin sulhu domin zamantakewar alummar wannan kasa.
Sai dai jammian diplomasiyya sun bayyana tsoronsu na yiwuwan gwamnatin na Gnassimbe,dangane da bukatun yan adawan na soke wannan sakamako ko kuma sake gudanar da sabon zabe a wannan kasa.
Sakamakon zaben na nuni dacewa Gnassimbe ya lashe wannan zabe da sama da kashi 60 cikin 100,ayayinda Dan adawa Emmanuel Akitani-Bob ya samu kashi 38 daga cikin dari.
Magoya bayan jammjiyun adawan wannan kasa dake yammacin Afrika dai sun lashi takobin cigaba da adawa da mulkin Gnassimbe,abunda suka bayyana da kasancewa doriya kan mulkin danniyar mahaifinsa tsohon shugaba kuma marigayi Gnassingbe Eyadema.Togon dai ta fada hali na tsaka mai wuya bayan mutuwan Eyadema a ranar 5 ga watan Febrairu.Saoi kalilan bayan mutuwan nasa ne aka sanar da nadin Dansa Faure mai shekaru 39 da haihuwa a matsayin magajin wannan mukami,saboda gudun fadawar kasar rikicin siyasa,amma korafe korafe daga kasashen ketare da zanga zanga cikin kasa ya tilasta shi sauka daga wannan mukamin.
A yanzu haka dai hukumar yan gudun hijira ta mdd ta sanar dacewa komai ya fara lafawa a wannan kasa,kana an daina samun karuwan yan gudun hijira daga Togon zuwa janhuriyar Benin da kuma Ghana dake makwabtaka da ita.Ayayinda wasu yan gudun hijiran tuni suka fara komawa gida,wasu kuwa na muradin hakan.