Rikicin PDP ya ɗauki wani sabon salo
September 6, 2013Mataki da shugaban kwamitin amintattu na jami'yyar ta PDP ɓangaren Bamanga Tukur din ya ɗauka na laƙabin ake yiwa PDP da sunan tsohuwa. Chief Tony Anenih a fili yake nuna bacin ran wasu daga cikin jiga-jigan ya'yyan jami'yyar da ke ɓangaren shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. A kan chief Anenih ya yi gargaɗin cewar Alhaji Bamanaga Tulur ɗin na rusa ƙoƙarin sulhu ne a mumunar ɓarakar da ta afkawa jam'iyyar.
Jayayya na ƙaruwa tsakanin 'yan jam'iyyar ta PDP.
Wannan ya nuna cewa sannu a hankali dai kalo na ƙara komawa sama domin inda hankali ke ƙara karkata a kan rawar da Alhaji Bamanga Tukur ke takawa a wannan rikici a matsayinsa na shugaban jam'iyyar. Barazanar da ya yi ga masu riƙe da muƙammai kuma suka ɓalle zuwa ɓangaren da suka kira da sabuwar PDP ya sanya Hon Musa Sarkin Adar ɗaya daga cikin 'yan majalisar da suka ɓalle zuwa sabuwar PDP ya bayyana cewa.
''Tsarin mulkin ƙasar ya bai wa kowa damar komawa wata jam'iyya in yana so, haka nan kuma ko an zaɓeka in kana riƙe da wani muƙami ko ɗan majalisa ne ko shugaban ƙasa to kana nan a kan wannan muƙami ko da ka canza jam'iyya. Ba irin zaɓe na jam'iyya ba ne, to tashi dokar ce zai yi amafani da ita? Abin da yasa muka yi tsaye a kan wannan duk jama'ar Najeriya suna ganin jam'iyyar PDP ta ɗauko Salo irin na kama karya kamar irin jam'iyyar Baaths ta ƙasar Iraqi da na ƙasar Italiya wanda shugaba ke ɗaukan kansa Kaman shi ne ƙasar. In ka fadi ra'ayi wanda bai yi dai dai da na shi ba, ka yi laifi ga dokar ƙasa.''
Ga Alhaji Abubakar na hannun dama Alahaji Bamanga Tukur yace akwai fa buƙatar fahimtar matsayin da ta Alahaji Bamanga Tukur ya ɗauka a kan wannan rikici.
''Bamanga bai da wani laifi gare su sai kawai ya fito don ya faɗa masu gaskiya Bamanga shi ke son ya shinfiɗa dimokraɗiyya a Najeriya don haka muka ga ya dace ya zo a yi tafiyan nan tare das hi, wancan lokaci ai kowa ya san Bamanga na cikin mutanen da ake kalonsu a arewa. Duk wani dan Najeriya dan jam'iyyar PDP ya kamata yana biyayya ga Bamanga.''
A yayinda tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yake can yana jagorantar ƙoƙarin sulhunta ɗaukacin ɓangaren da ke jayaya da juna a kan dagewar lallai sai an sauke Alha Bamaga Tukur daga kan shugabancin jam'iyyar, kuma shugaban Najeriyar ya cika alƙawarin da suke iƙirrarin ya ɗauka na cewa ba zai tsaya takara a 2015 ba, ga Yarima Tafiɗa Mafindi wakili a kwamitin zartaswar na jam'iyyar na mai cewa duka ɓangarorin dai ba za su so ganin maimaita abin da ya faru a shekarun baya a fagen siyasar Najeriyar ba.
Fatan samun daidaituwa a rikicin na PDP
''Mun san abin da ya faru a 1984 inda usur aka busa ka ce kowa ya kai kansa gidan yari ko ofishin ‘yan sanda wa zai yarda wannan ya sake samunsa, wanene cikin gwamnonin Najeriya wanda ba shi da laifi yasa zai ɗauki dutse ya jefawa mai laifi? Amma tunda siyasa ake yi kowa kuma ya san inda marace zai yi mashi ai dole a shirya.'' A yayinda har yanzu ba'a fitar da fata ba a kan yiwuwar sassanta wannan rikici, a bayyana ta ke a fili cewa rikicin na ci gaba da ɗaukan sabon salon a bazatta. Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a yunƙurin sulhun da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ke yi, mutumin da babu wanda ke ja da tasirinsa a jam'iyyar PDP da ma fagen siyasar Najeriya, duk kalonsa a matsayin mazari babu wanda ya san gabansa.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane