Rikicin PDP na ɗaukar sabon salo
February 28, 2013A wani abun dake zaman kama hanyar bude sabon babi a cikin rikicin jamiyyar PDP mai mulki a cikin tarrayar nigeria, an fara kace nace da musayar yawu game da makomar takarar shugaban kasar da jamiyyar sa ta PDP tace yana da yancin yi a cikin ta.
Sannu a hankali dai iskar na kara karfi sannan kuma guguwar na kara nisa da zumbutun kaza a cikin jamiyyar PDP da ta dauki tsawon lokaci tana jan kafa amma kuma ta fito ta tabbatar da takarar shugaban nigeriar Goodluck Ebele Jonathan.
To sai dai kuma daga dukkan alamu tun ba a kai ko ina matsayin shugabancin jamiyyar da ake yiwa kallo na hannu gas daman shugaban dai na neman hargitsa lamura a cikin PDP da ta dauki tsawon lokaci tana ganin ba dadi a tsakanin yayanta.
Duk da cewar dai bai fito fili wajen yanke hukuncin karshe game da makomar tikitin shugaban kasar na jamiyyar PDP ba ana dai kallon kalaman na Bamanga tukur a matsayin kokari na tabbatar da tazarcen ta shugaba jonathan a nan gaba.
Abun da kuma tuni ya fara caja kwakwalwar yayan PDP na arewa da ke gwagwarmayar neman sauyi da kuma ke tsaye kan dagewar wa'adi daya tilo ga shugaban kasar.
Bello Sabo Abdulkadir dai na zaman sakataren kungiyar dattawan PDP na arewa kungiyar kuma da shekaru biyun da suka gabata ta kai ga tsaida Alhaji atiku abubakar domin gwada kwanji da Jonathan yayin zaben share fagen jamiyyar. Kuma a cewar sa a wannan karo zabi a garesu na zaman yiwa jamiiyar kaura domin yakar burin na shugaban kasa.
Rungumar jamiyya ta adawa ko kuma tunkarar Jonathana a cikin jamiyyar PDP dai an share kusan wattani biyun da suka gabata ana kace nace da musayar yawu da nufin tabbatar da ikon na jonatahan kan kowa a cikin PDP.
Abun kuma da ya kai ga haihuwar sabuwar kungiyar gwamnonin jamiyyar tare kuma da tabbatar da shugabancin na hannun daman shugaban kan shugabancin kungiyar amintattun jamiyyar.
Ko bayyanan dai kuma su kansu gwamnonin dake adawa da burin na jonathan dai sun fara korafin bita da kulli a bangaren jamian tsaron da a cewarsu ke da goyon bayan fadar ta shugaba jonathan. A wani abun dake zaman alamu na murde wuya da nufin cika burin gwamnatin.
To sai dai kuma a cewar Hon Bala Bawa kaoje matakan da take dauka na zaman na kokarin tabbatar da karfin jamiyyar ne dake fuskantar kari na adawa maimakon zama yan amshin shata ga shugaban kasar.
Mafita ga arewa a jam'iyyar PDP
Babban mafita ga arewa a jamiyyar PDP ya zuwa yanzu dai na zaman fakewa bisa rikicin kundin tsarin mulkin kasar da ya tanadi rantsuwa har sau biyu maimakon uku ga jonathan din da ya rantse har sau biyu ke kuma kama hanyar fuskantar ta uku.
Rikicin kuma da a cewar ali ahmed gulak dake baiwa shugaban kasar shawara kan harkar ta siyasa ba abun hana bacci bane ga shugaban kasar.
Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin a tsakanin yan jamiyyar da ta kira kanta mafi girma a nahiyar africa sannan kuma tafi kowace rikici a cikin nahiyar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Saleh Umar Saleh