1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin PDP na karuwa duk da kokarin yin sulhu

January 3, 2014

Wannan sabani na cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta ya sanya da yawa daga cikin 'ya'yanta suna canja sheka zuwa bangaren 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/1Al2E
Nigeria Tag der Demokratie
Hoto: DW/U. Musa

Duk da cewa tsaffin jiga-jigan jam'iyyar PDP da kuma mataimakin shugaban Najeriya Architect Namadi Sambo, a wannan makon sun yi korarin dinke babbar barakar da ke addabar jam'iyya a ziyarar da ya kai Kaduna, amma har yanzu rikicin jam'iyyar PDP a birnin na Kaduna da ma wasu jihohin arewa sai kara habbaka yake wanda ya sanya wasu 'yan jam'iyyar canja sheka zuwa APC.

Alhaji Adamu Usman Balarabe wani jigo ne a karkashin jami'yyar PDP a Kaduna daga Zaria, da shi da wata tawagarsa ta 'ya'yan PDP sun je shelakwatar babbar jam'iyyar adawa ta APC a Kaduna inda ya bayyana kudurinsa na canja sheka zuwa APC. Wannan al'amari na canjin sheka da 'ya'yan jam'iyyar PDP da ma tsaffin shugabanninta ke yi a kullum na zama wani babban kalubale wanda ke bukatar daukar kwararan matakai domin shawo kansa.

Matakan warware matsalar PDP

Barista Lawal Baba Aliyu shi ne tsohon sakataren Jam'iyyar PDP a yankin arewa maso yamma da ke cewa: "wannan rikici da jam'iyyarsu ke fuskanta, abu ne da ke matukar bukatar daukar matakan dakile ci-gabansa, bisa la'akari da irin matsalolin da yake janyo wa jam'iyya. A saboda haka ne ma, muka gudanar da babban taro a Kaduna tare da mataimakin shugaban kasa domin fara daukar matakan magance abubuwan da ke addabar jam'iyyarmu a cikin wannan kasa da ke da dunbun masoya."

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Rahotonnin sun nunar da cewa zuwan mataimakin shugaban kasa Architect Namadi Msambo, Kaduna a cikin wannan makon domin magance matsalolin da ke ci wa jam'iyyar tuwo a kwarya, babu abunda ya haifar illa kara matsaloli, domin ko a kwanaki ukun da suka gabata sai da 'yan jam'iyyar PDP daga yankin kudancin Kaduna sama da 2,300 suka canja sheka. Haka zalika, rahotannin sun nunar da cewa, a ranar Alhamis ma an kara samun wasu dake da yawan 1,200 kuma ana samun karuwar masu shiga wannan sabuwar jam'iyya ta APC.

Alhaji Yaro Koka Kola shi ne tsohon shugaban jam'iyyar CPC a Kaduna wanda kuma yana daga cikin shugabannin sabuwar jam'iyyar APC a Kaduna da ke tarbar wasu 'ya'yan jam'iyyar PDP a lokacin da suka shiga sabuwar jam'iyyar:

"Muna masu barka da zuwa da lale marhabin da shigowarsu wannan sabuwar jam'iyya mai kare hakkin kowane dan Najeriya, ba tare da nuna wani bambamci ko bangaranci ba. A saboda haka jam'iyyar APC ta kowa da kowa ce, dake bukatar ganin an sami sabuwar hanyar ci-gaban mulkin siyasa a cikin wannan kasa."

Rashin kishin jam'iyya ya kawo canja sheka

Honorable Hassan Jumare, dan majalisar dokokin Jihar Kaduna ne daga PDP wanda kuma ya kasance daya daga cikin masu kishin PDP a Kaduna cewa yayi "dukkanin masu yin gudun hijira daga jam'iyyarsu zuwa APC ba masu tawakkali ba ne da Allah. Kuma idan har sun manta, PDP ce ta taimaka masu suka kawo inda suke, da suke tayar mata da hankali. A saboda haka muna fatan dukkanin wadanda suka gudu daga wannan jam'iyyar kada su manta da cewa, PDP ita ce kadai jam'iyyar da za ka yi gudun hijira, bayan ka dawo ta karbe ka da hannu-bi-biyu."

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Dr Hakim Baba Ahmed shi ne shugaban jam'iyyar APC a Kaduna wanda ya bayyana wa manema labarai cewa a wasu makonni masu gabatowa za su yi gangamin tarbar 'ya'yan PDP dake da yawan gaske.

"Shirye-shiryen karban wani babban tawaga ta PDP a Kaduna sun kammala, kuma muna son talakawa da sauran bayin Allah su sani cewa babu gudu, babu ja da baya, lokaci ya yi na canja salon mulkin demokuradiyya a cikin wannan kasar domin bai wa kowane dan Najeriya damar fitowa a fafata da shi."

Duk da cewa masana kan harkokin siyasa a Najeriya sun nunar da cewa zaben shekara ta 2015 dai, zabe ne da za a fafata tsakanin PDP da APC.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mohammad Nasiru Awal