1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin PDP a Najeriya na ƙara rincaɓewa

October 11, 2013

Ɓangaren sabuwar jam'iyyar PDP da ya ɓale ya ce ba zai ja da baya ba, daga gwagwarmayar da yake yi.

https://p.dw.com/p/19yLs
Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Hakan kuwa ya biyo baya sanarwa da hukumar zaɓe ta ƙasar ta bayyana cewar ɓangaren jam'iyyar PDP da ke ƙarƙashin jagorancin Kawu Baraje ba hallatace ba ne. To ko wane tasiri zai yi a ƙoƙarin sulhun da ake yi a jam'iyyar da ke mulki a Najeriya.

To bugu biyu dai suka sha a lokaci guda a kan gwagwarmayar da suke yi da ta sanya su ɓalewa da ma sanar da sabbin shugabanisu. To kuwa baya ga fitowar da hukumar zaɓen ƙasar mai zamna kanta ta yi na bayyana rashin hallarcin shugabancin ɓangaren Abubakar Kawu Barajen da ake yi wa laƙabi da sabuwar PDP. Sakamakon shari'ar da suka shigar a gaban kotu a Lagos a kan wannan batu da masharahnata ke ganin koma baya ne ga gwagwaryar ta su.

Hukumar zaɓe ta Najeriya ta ɓangaren Kawu Baraje ba ya da gasgiyya.

Ganin wannan hali da suka samu kansu musamman matakin da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗauka a wacce aka bai wa hurumi sa ido a kan yadda jam'iyyyun siayasa ke gudanar da harkokinsu a Najeriyar. Ko a yanzu za su haƙura kenan daga wannan gwargwamaya da ke ƙara yin ƙarfi wacce gwamnonin bakwai na jam'iyyar ke yin-ja-in-ja. Alhaji Nasiru Isah Abubakar shi ne sakataren tsare-tsare na ɓanagren jam'iyyar

Wahlplakat von Dr. Bamanga Tukur, Präsident der PDP ,( Partei an der Macht in Nigeria) Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

Ya ce : ‘'Na farko dai hukumar zaɓe ba ta da hurumin ta amince ko rashin amincewa da wani ɓangare na jam'iyya, saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da dama a yi ɓangare a jam'iyya.''

Tuni da daɗewa dai ɓangaren jam'iyyar PDP na Bamanga Tukur ke ɗaukan matakai a kan na Kawu Barajen, na baya-baya a cikinsu shi ne kafa kwamitin ladabtar wa. To sai dai matakin da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗauka a yanzu ya sanya ɓangaren Bamanga Tukur na PDP bayyana cewar gaskiyya ce ke yin halinta. Barrister Abdullahi Jallo shi ne mataimakin sakataren yaɗa labaru na jam'iyyar PDP ɓangaren Bamanga Tukur.

Ya ce :‘'Abin da hukumar zaɓe ta yi ta jadadda abin da yake doka ne domin abin da yake faruwa shi ne idan ɗan jam'iyya ce da ba ta a kan mulki in ka yi ɓangare ,za'a yarda da wannan har ka yi ta ja. KAmar yadda ya faru a jam'iyyar APGA.''

Babu alamun samin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu

Bisa la'akari da cewa wannan rikita-rikitar na faruwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙokarin sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu da ke ci gaba da yin tankiya , tuni masharahanta suka bayyana cewar wannan lamari zai shafi ƙoƙarin sulhun da ake yi. A yayin da masharhanta ke nuna damuwa a kan illar da wannan lamari ka iya yi a kan ƙoƙarin sulhun da ake shirin komawa bayan bikin sallah, ga ɓangaren jam'iyyar PDP na Abubakar Kawu Baraje na mai bayyana cewar sun gano inda aka dosa a kan batun sulhunta rikicin jam'iyyar.

Auf dem Bild: Parteizentrale PDP (Partei an der Macht in Nigeria) in Abuja, Nigeria. Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Cibiyar jam'iyyar PDPHoto: DW/U.Haussa

Ya ce : ‘'Gaskiya Magana shi ne yaudara ce ba sulhu ba, saboda idan ka kawo ma mutum abubuwa takwas kace ina son ka duba domin waɗannan sune buƙatuna kafin mu yi sulhu.Ka ga yin haka ya zama kuma wani abu na da daban na bani gishiri na baka manda.''

Wannan rikici na cikin gida ga jam'iyyar PDP da ake yin sa bisa ga kokuwar ka iwa ga madafan iko a zaɓen 2015 na kasance wa wanda ke ci gaba da yin tasiri ga jam'iyyar da ma demokraɗiyyar Najeriya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris

Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani