1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin mulki a jam'iyyar PDP

March 5, 2012

Rabon muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin magoya bayan jam'iyyar PDP dake mulki a Najeriya

https://p.dw.com/p/14FVM
Bildausschnitt von Jonathan Goodluck. French Prime Minister Francois Fillon, left, stands with Nigerian d Vice President Goodluck Jonathan as he meets for talks with leaders of Africa's most populous nation, at the Presidential Villa in Abuja, Nigeria Friday, May 22, 2009. Fillon later told reporters that France was Nigeria's second-largest investor after the United States, and he praised Nigeria for contributing to peacekeeping missions across Africa. (AP Photo/Abayomi Adeshida)
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP

A wani abun dake zaman alama ta ɓarkewar gwagwarmayar ikon da ake ta'allakawa da zaɓukan shugaban ƙasar na shekara ta 2015, a karon farko an gaza kaiwa ga sulhu tsakanin PDP da a al'adance kan kashe ta sha romo a tsakanin shugabannin ta.

An dai ƙare makon jiya tare da kaiwa harga baiwa hammata iska a ƙoƙarin zaɓar shugabannin da za su ja ragamar jam'iyyar PDP a matakan unguwanni da ƙananan hukumomin jihohin ƙasar.

Ana ganin jammiyar PDP mai taken mafi girma a nahiyar Afirka da kuma daga dukkan alamu ke ƙara shiga duhu da sarƙaƙiya ga ƙoƙarin neman fitar da shugabanni a matakai daban daban na jam'iyyar.

Zaɓen 2015 ne tushen rikicin PDP a yanzu

PDP da ta ware ranar 24 ga wannan wata da muke ciki domin taro na ƙasa dai ya zuwa yanzu na cikin tsaka mai wuya a ƙoƙarin ta na kaiwa ga kammalla tarukan dama fitar da shugaban da ake fata zai kai ga jam'iyyar ya zuwa zaɓukan ƙasar na shekara ta 2015 cikin nasara.

Babban ƙalubalen dake barazanar raba kan jam'iyyar dake da 'yan takara kusan 12 ga kujearar shugabancin jam'iyyar kaɗai.

Ana dai kallon gwagwarmayar zaɓen shugaban ƙasar na shekara ta 2015 a matsayin ummul aba'isin rikicin da ta kai ga kafa tanti a tsakanin 'yan takara a ɓangaren masu ruwa da tsaki da neman shugabancin ƙasar.Ya zuwa ranar yau dai ana Ambato aƙalla 'yan takara biyar da suka haɗa da Alhaji Bamanga Tukur dake zaman tsohon minister kuma gwama a tsohuwar jihar Gongola da yanzu haka kuma ke nuna alamun samun ɗaurin gindin fadar shugabn ƙasar ta Aso Rock.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh