Rikicin Libiya na kara kazancewa
October 20, 2014Al'ummar Libiyan dai sun gudanar da juyin juya hali a kasar wanda ya yi awon gaba da kujerar mulkin sama da shekaru 40 na tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi bisa fatan da suke da shi na bude sabon babi. Wannan fatan nasu dai ya rikida zuwa rikicin siyasa. To sai dai mafi yawan matsalolin da al'ummar ke fiskanta su suka kirkiro su da kansu.
Wa ke da alhakin juyin-juya hali a Libiya?
Ba matasa ne ke da alhakin juyin-juya halin ba, su kansu ba za su iya yin irin wannan abun ba, sun sha kwaya ne wanda suka samu daga hannun kungiyoyin 'yan tawayen da ke da alaka da kungiyar al-kaida, abin da marigayi Kanar Mu'ammar Gaddafi ya rika cewa ke nan, a wancan lokacin da aka kaddamar da zanga-zanga ta farko da ta fara barazana ga mulkinsa na sama da shekaru 40. Amma duk da cewa masu zanga-zangar sun karyata hakan, wannan bai sanya Gaddafi yin kasa a gwiwa ba a shekarar ta 2011 ya yi amfani da karfin tuwo a kan duk masu tayar da kayar baya kuma dubbai sun rasa rayukansu ga ma irin kalaman da ya rika fada a wancan lokaci.
Fada ya kara rincabewa musamman a yankin gabashin kasar bayan da 'yan tawaye suka karbe jagoranci a lardin Kyrenaika, suka kuma kutsa yankin yammacin kasar inda dakarun Gaddafi suka ci karfinsu, daga nan ne a watan Maris dakarun Gaddafi suka fara mayar da martani kakkausan gaske, har sai da 'yan tawayen suka yi kira ga al'ummar kasa da kasa da su kawo musu dauki shi kuma kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya nan da nan ya zartar da kudurin 1973 wanda ya bukaci tsagaita wuta da kuma kai hari ta sama. Daya daga cikin filayen daga na karshe kafin mutuwar Shugaba Gaddafi shi ne Sirte mahaifarsa, inda a nan ne ranar 20 ga watan Oktoba wutar yakin ta rutsa da shi ya kuma fada hannun 'yan tawayen, da yake yunkurin tserewa.
Rashin samun nasarar zabe ya janyo rikici
Bayan zaben majalisar dokokin da aka gudanar a watan Yuni, wasu 'yan tawaye, wadanda wakilan da suka gabatar wajen takara ba su yi nasara sosai ba, sai suka yi kokarin janyo matsala a birnin Tripoli, suna masu cewa daga yanzu su za su rika dora wakilansu abin da ya sanya sauran 'yan majalisar sauya matsuguni zuwa Tobruk wanda ke da tazarar kilomita 1000 daga Tripoli suka kuma bukaci tallafin Majalisar Dinkin Duniya wajen kawo karshen wannan rikicin da ke barazanar raba kasar. Ziad Akl jami'i a cibiyar Al-Ahram da ke Masar, wadda ke nazarin siyasa na ganin wannan yanayi na da alaka da ta'addanci sai dai har yanzu abubuwa kokarin farawa suke kuma za a iya cin karfinsu.
A yanzu haka dai kasar Masar na taimakawa, kuma bisa dukkan alamu rikicin Libiyan zai dauki lokaci kafin a iya shawo kan shi musamman a daidai wannan lokacin da abubuwa kamar barazanar yaduwar cutar Ebola, da rikicin Ukraine da kuma barazanar kungiyar IS a kasashen Siriya da Iraki ke daukar hankalin al'ummar duniya.