Takun saka kan 'yan takara a manyan jam'iyyun Najeriya
September 25, 2018Ya zuwa yanzu dai an tsara kammala tantace 'yan takara na shugabancin kasa 13 da ke neman fafatawa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ta adawa.
To sai dai kuma tuni wani sabon rikici na neman barkewa sakamakon yanke hukuncin daukar babban taron jam'iyyar ya zuwa a Fatakwal fadar gwamnantin Jihar Rivers da ke zaman manya na cibiyoyin jam'iyyar.
Kama daga shugaban jam'iyyar Uche Secondus ya zuwa babban jagoranta Nyesom Wike dai Fatakwal din dai na zaman gida na samun sauki dama kila kai wa ya zuwa taron na shida ga watan gobe na Oktoba a cikin sauki.
Sai dai kuma ga da dama na shugabannin jam'iyyar dai birnin Fatakwal din na zaman wani dandali na murdiya da son rai da kila ma hana dama ta da dama ga masu tunanin Wike din yafi karkata zuwa ga daya a cikin daya a cikin yan sauyin shekar jam'iyyar.
Dr Umar Ardo dai na zaman daya a cikin masu neman takarar neman gwamnan Jihar Adamawa a cikin jam'iyyar 'yan lemar kuma a fadarsa sau biyu PDP na taro a Fatakwal sau biyun kuma tana karewa a cikin son rai sakamakon son zuciya ta Nyesom Wike.
Barazana ga ruhin lema ko kuma kokari na siyasar son rai dai, makonni biyun da ke tafen na da tasirin gaske a cikin makoma ta siyasar Najeriya, kuma na shirin zaman damar karshe ga da dama a ciki na masu takarar PDP da ko dai ke shirin cika saba'in a duniya ko kuma ke tunkarar saba'in din yanzu. Makonnin biyu dai na nufin samun dama ta takara ko kuma ritayar dole karkashin tsarin karba-karba na siyasa a tsakani kudu da arewacin Najeriya.
To sai dai kuma ko bayan 'yan lemar ga su kansu masu takama da tsintsiyar dai rudanin bai kyale ba, domin kuwa sau dai dai har guda uku jam'iyyar na saka ranar zaben fidda gwani na shugaban kasar sau ukun kuma tana kai wa ga dagewa a wani abin da ake ta'allakawa da rigimar tsarin zaben jam'iyyar.
APC dai na rabe a gida biyu a tsakanin masu goyon gwajin farin jini da ke cewar a yi ta a bude da kuma masu fadin sannu-sannu kwana nesa da ke neman bin tsohon tsari na wakilai.
Ana dai kallon makonni biyun da ke tafe na da babban tasirin da ke iya kawo sauyi mai nisa a daukacin fagen siyasar Najeriya.