1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin cikin gida na kara kamari a PDP

April 17, 2013

Fadar shugaban Najeriya ta mussanta zargin da ake wa Goodluck Jonathan na fara yakin neman zaben shekarar 2015.

https://p.dw.com/p/18HOO
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

A wani abun dake zaman alamu na kara rudewar al'amura a cikin jami'yyar PDP mai mulkin Tarayyar Najeriya, a na cigaba da kwan gaba kwan baya tsakanin fadar gwamnatin kasar da tace bata da buri na sake takarar har yanzu, amma kuma ake mata zargi da kokari na ganin baya ga gwamnonin kasar dake sunsunar shiga cikin ta a zabukan na gaba.

Can a gidan Wadata dai uwar jam'iyyar PDP ce ke bikin rantsar da sabbabin shugabanni fil dinsu ga reshen jihar Rivers Na jam'iyyar a wani abun da ke zaman cigaban yakin cacar baka a tsakanin fadar gwamantin kasar da kuma gwamnan jihar Rotimi Amechi,sai kuma fadar ta Aso Rock inda kakakinta ke rantsuwa kan cewar mai gidansa Dr Goodluck Ebele Jonathan bai kafa wani kwamitin yakin neman zaben sa a shekara ta 2015 kuma baya goya baya kan kowa da nufin cimma buri na siyasa a kasar a wani abun dake zaman alamu na kara rudewar harkokin PDP dake kara shiga duhu tana ikiraren haske.

A cikin bacin rai ne dai fadar gwamnatin tace bata umarta ba, ba kuma tada hannu a cikin sabon rikicin siyasar kasar ta Najeriya, sannan kuma tana ahir ga duk wasu masu amfani da sunan shugaban da nufin jefa shi cikin rikicin siyasar kasar ko kuma cimma biyan tasu bukatar.Abun kuma da a cewar kakakin fadar Rueben Abati shugaba Jonathan ba zai lamunta ba ko kadan.

Nigerian incumbent President Goodluck Jonathan cast his ballot in Otuoke, Nigeria, Saturday, April 16, 2011. Nigerians chose their president in an election Saturday many hoped would show how Africa's most populous nation could hold a credible vote without the violence and rigging that marred previous ones, though children cast ballots and party officials helped others press their inked fingers to paper. (AP Photo/Godwin Omoigui)
Hoto: AP

"Shugaba Jonathan bai amince da takarar ko burin wani mutun na zabe a shekara ta 2015. Haka kuma bai umarci wani yi masa yakin neman zaben tasa takarar ba. A matsayin sa na shugaba mai bin doka shugaba Jonathan yayi imani da dokokin Hukumar Zabe da jam'iyyun siyasa na zaben dan takarar kowane zabe.

A matsayinsa na dan kasa mai bin doka shugaba Jonathan ba zai yi duk wani abu a fili ko a kaikaice ba, da ya sabawa dokoki.

Saboda haka shugaba Jonathan na raba kansa da duk wani mai amfani da sunansa don tsayawa takara ko kuma fara yakin neman zabensa na shekara ta 2015.

Ana dai cigaba da kai gwauro da mari da nufin hade kan 'ya'yan jam'iyyar PDP dake rabe a tsakanin kungiyar gwamnoni da fadar gwamnatin kasar da kuma ke fuskantar barazana mafi girma ta asarar kujerar mulkin kasar a karon farko tun sake dawowar demokaradiya a Najeriya.

To sai dai kuma babban matsalar na zaman ta buri dama gwagwarmayar mallakar ruhin jam'iyyar ya zuwa ga zabukan na shekaru biyu masu zuwa.

Burin kuma da ya kai ga PDP kokarin rage karfin gwamnonin sannan kuma ke neman kawo karshen shugabancin shi kansa shugaban jam'iyyar na kasa.

epa03046192 (FILE) A file photograph Nigerian president Goodluck Jonathan (2-L) standing on the back of a vehicle as he is driven after he was sworn in as president during a ceremony in Abuja, Nigeria 29 May 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/STR *** Local Caption *** 00000402757844
Hoto: picture-alliance/dpa

Alhaji Sule Lamido dai na zaman gwamna ga jihar Jigawa daya kuma daga cikin gwamnonin da ke kan gaba a kokari na adawa da rage karfin gwamnonin jam'iyyar da nufin bada damar sake takara ga shugaban kasar kuma a fadarsa ba gudu ba kuma jada baya ga duk wani kokari kyale gwamnonin a inda suke a yanzu.

Ana dai kallon takarar ta Lamido da Rotimi Ameachi da zai taimaka masa a matsayin barazana mafi girma dake gaban fadar ta Aso Rock ya zuwa yanzu.

Mawallafi:Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi