Rikicin Burma
September 26, 2007Ayayinda komitin sulhu na mdd ke shirin gudanar da taro na musamman adangane da halin da ake ciki a kasar Burma,ko kuma Myammar,rahotanni na nuni dacewa jamian tsaro sun bindige biyar daga cikin masu zanga zangar adaw da gwamnati a babban birnin kasar dake Rangoon.Bugu da kari an cafke akalla mutane 200,ayayinda ake cigaba da harbin barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu boren,wadanda sukayi watsi da umurnin gwamnati na zama a cikin gidajensu.Wadanda suka ganewa idanunsu wannan rikici,sun shaidar dacewa jamian tsaro na cigaba da dukan sanannun malaman addinin Bhuda da ake darajawa a kasar ta Burma,tare da durasu acikin motoci domin tafiya dasu wurin da zaa tsare su.Ayau ne dai aka shiga yini na tara a jere ana wannan zanga zangan adawa da gwamnatin sojin wannan kasa ,wanda ke zama mafi munin irinsa a shekaru 20 da suka gaba a wannan kasa.