1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya rincabe a PDP mai mulki

May 28, 2013

Dattawan PDP sun shiga yunkurin ceto jam'iyyar daga rudanin da ta shiga sakamakon rikicin zaben shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya

https://p.dw.com/p/18frs
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

A wani abun da ke zaman alamun kara shiga duhu da karatun rudu, manyan dattawan Jam'iyyar PDP mai mulkin Tarayyar Najeriya sun fara kiran neman hanyar ceto jam'iyyar da sannu a hankali ke dada fuskantar rikici a tsakanin 'ya'yanta.

An dai yi mata ginshiki da kwangiri karfen jirgi an kai ga kiranta da a kori sojan Tarayyar Najeriya, ga jam'iyyar PDP mai mulkin da ta share shekara da shekaru ta na cin karenta babu babbaka, amma kuma 'yan hanjin cikin ta ke kokarin rushewa.

Tuni dai tsoro ya kai ga har a cikin zuciyoyin manyan iyayen da su ka hadu su ka kai ga kafa ta shekaru 15 din da su ka gabata, yanzu haka kuma rikicin da ta fada ya sa su fara tunanin ta zo karshe.

Dakatar da gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi ta zamo tsumangiyar kan hanyar da ta tada kowa bacci a cikin PDP da kuma a cewar tsohon mataimakin shugaban kasar kuma jigo a cikinta lokaci yayi na sake taruwa da nufin ceto jam'iyyar.

national assembly.jpg
National Assembly AbujaHoto: DW

Ta yi baki tai daci dai a cikin PDP a fadar Atikun da yace 'ya'yanta sun rabe gida-gida, kuma tana fuskantar babbar barazana ga makomar demokaradiyyar kasar.

Kalaman na Atiku dai na zuwa ne a daidai lokacin da al'amura ke kara rudewa a cikin jam'iyyar da yanzu haka 'ya'yanta biyu ke ikirarin shugabancin kungiyar gwamnonin kasar mai tasiri amma kuma ta kai ga azarbabin dakatar da guda ba ba'asi.

Duk da cewar dai ta fito tace bulaliyar kan gadon bayan Rotimi Ameachi, bata ruwa balle tsaki da maganar shugabancin kungiyar dai tuni gwamnan Jihar Rivers yace 'yan PDP na Abuja dai na barazana har ga rayuwarsa bisa rikicinsa da babban dodon fadar gwamantin kasar ta Aso Rock.

Abun kuma da daga dukkan alamu ya harzuka jam'iyyar da ta zarge shi da kokarin shafa mata kashin kaji a cikin abun da bata san da zaman sa ba yanzu haka.

"Honorable" Bala Kaoje na zaman ma'ajin jam'iyyar na kasa daya kuma daga cikin wadanda su ka zauna su ka ce tsagerancin na Ameachi ya kai ga tura shi hutun dole da nufin tabbatar da hankali kansa.

Gyara a cikin PDP ko kuma gyara irin na ganga ta auzunawa dai ko bayan rikicin na Ameachi dai dama PDP na fama da rikicin cikin gidan da ya kai ga rabuwar kan 'ya'yanta da kuma kasa kiran taron majalisar zartarwarta shekara kusan guda bayan sake zaben shugabanninta.

To sai dai kuma tuni ran su kansu 'yan jam'iyyar ya kara baci da matakin da wasunsu ke yiwa kallon kokari na a fasa kowa ya rasa a bangaren shugabancin jam'iyyar dama fadar gwamnatin kasar da sannu a hankali tauraruwarta ke dusashewa cikin kasar.

President Goodluck Jonathan arrives for the ruling party primary in Abuja, Nigeria, Thursday, Jan. 13, 2011. Delegates of Nigeria's ruling party began voting Thursday night to pick its presidential candidate, choosing between honoring a power-sharing agreement by selecting a Muslim or endorsing the oil-rich nation's current Christian leader. (AP Photo/Sunday Alamba)
Goodluck JonathanHoto: AP

Alhaji Bello Sabo Abdulkadir, na zaman Sakataren tsohon Kwamitin da ya kai ga fitar da dan takarar sulhu ga arewacin Tarayyar Najeriya a lokutan fidda gwanin jam'iyyar na zaben shugaban kasar shekara ta 2011 kuma a fadarsa babu adalci ba kuma tsoron Allah ga tunanin dattawan PDP.

Abun jira a gani dai na zaman makomar jam'iyyar da shugabanta ke shirin fadawa 'yan kasar abun da ya kulla cikin tsawon rabin wa'adin mulkinsa na shekaru hudu.

Mawallafi:Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi