1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya mamaye taron kasa a Najeriya

Mohammad AwalMarch 27, 2014

kura da siyasa na neman kunno kai tsakanin Kudu da Arewa a zauren taron kasa bayan share kusan makwanni biyu ana gudanar da shi a birnin tarayya wato Abuja.

https://p.dw.com/p/1BWnr
Hoto: DW/U. Musa

Wakilai a taron kasa sun kai ga share kwanaki 10 cikin 90, sun kuma kai ga lamushe miliyoyi na kudin talakawan tarayyar Najeriya. To sai dai kuma sun gaza kaiwa ga ko'ina. Maimakon haka ma sannu a hankalitaron ne neman rikidewa ya zuwa fage na yakin yanki.

An share kwanaki uku ana fafatawa da nufin yanke hukuncin da ta kai ga daukar kuduri a tsakanin wakilan kudancin kasar 280 da ke neman sai an sassauto ya zuwa biyu a cikin uku a matsayin ka'idar abun da ake bukata don yanki hukunci. A daya bangaren kuma 'yan uwansu 212 da ke Arewa da ke kallo a kyale hukuncin kan kaso uku a ciki na hudu na zaman mafitar neman yanke hukunci kan komai.

Jan aikin da ke gaban 'yan taron kasa

Da kyar da gumin goshi ne dai wani kwamitin 'yan 50 da shugaban taron ya kafa ya ceto zauren daga rudanin da ya kai ga fara kiran darewar ita kanta kasar da nufin tabbatar da 'yancin kowa. Abun kuma dake nuna alamar jan aikin da ke gaban 'yan taron da ke cikin taron da zuciya daban daban, da ma gwamnatin da ke fatan samar da ginshika na sabuwar kasa daga zauren.

Karte Nigeria
Bangaranci ya hana ruwa a gudu a taron kasa

Masana sun fara hasashen tarwatsa taron na zaman mafi alfanu ga tarrayar Najeriyar da ke shirin fuskantar zabukan kasar a 2015 cikin hali na rashin tsaro da tashin hankali. Dr Haruna Yarima da ke zaman daya daga cikin mahalarta taron ya ce babu bukatar ci gaba da muhawarar da a cewarsa ke shirin karewa ba tare da tsinana komai ga' yan kasar dake da burin canji ba.

Wallahi tallahi sati mai zuwa in ba a kai ga fara samun masalaha ba, ina rokon shi shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tarwatsa wannan taron domin ba zai tsinana wa Najeriya komai ba”

Batutuwan da ke hana ruwa gudu a taron kasa

Muhimman batutuwa zafafa kama daga karin matakin yankuna shida a matsayin wata sabuwar gwamnatin da ke tsakanin ta jiha da ta tarraya ya zuwa hanya ta rabon kudin da ma ta mallakin albarkatu dai na cikin batutuwan da daga dukkan alamu ke iya kaiwa ga jefa kasar cikin wuta da zarar da ma ta samu. Abun kuma da a fadar Dr Garba Umar kari da ke sharhi bisa harkoki na siyasa da zamantakewa ke zaman muguwar rawa ga gwamnatin da tuni ta yi nisa a cikin ban hakuri da nufin tabbatar da kasancewar kasar wuri guda.

Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Ba a fara tabo batun kananan yara ba a taron kasaHoto: DW

Watsewar wannan taro ma shi ne a'ala tun da da ma munce wannan taro a wannan lokaci bai dace ba. Kuma idan ba'a yi wasa ba zai iya ta da batutuwan da zasu iya ta da fitinu a kasar ; nan ka ga da muguwar rawa gara kin tashi.

Tun ba'a kai ga ko'ina ba dai 'yan taron suka fara batun an kwanto kura kuma tabbatar da kaita gidan tsira na zaman wajibi a bangaren gwamnatin da a cewar Junaid Muhammed da shi ma ke wakiltar kano a cikin zauren taron ya kama hanyar tilasa kawo karshen zaman karya cikin kasar ta Najeriya.

“ Idan ana so na goyi bayan a rusa,a fara bari ta dire tukun mu ga inda maganar ta fita shege ka fasa. Mu gani kuma bayan wannan me za su fito su fada mana sannan kuma in an bar maganar haka za'a zo ana tambaya shin abubuwan da ake na rashin adalci ya za a yi da shi.”

Abun jira a gani dai na zaman mafita ta gaba ga masu shirin taron da ma gwamantin da hankalinta ke tashe tsakanin tsomin baki tare da rushe tasirin taron tare da kyale ya dauki kasar cikin wani sabon rudani.

Mawallafi: Ubale Musa daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe