Mali: Rikici tsakanin 'yan tawaye da gwamnati
December 23, 2022Shugabannin Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a Mali sun yi ikrarin cewa gwamnatin Bamako na yi wa yarjejeniyar zaman lafiya rikon sakainar kashi. Gamayayyar kungiyoyin ta zargi majalisar mulkin sojin kasa da rashin mutunta yarjejeniyar da kuma yin biris da batun tabarbarewar tsaro a wasu yankunan kasar.
A cikin sanarwar hadin gwiwa da gamayyar ta fitar, ta ce matakin janyewar zai fara aiki daga yanzu har zuwa lokacin da za su gana da masu shiga tsakani na kasa da kasa.
A shekarar 2015 ce dai bangarorin suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Aljeriya, wanda ya kawo karshen fada tsakanin dakarun Mali da kuma 'yan tawaye ciki har da ta Abzinawa ta CMA da ke neman dara kasar gida biyu. Sai dai kasar ta ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyin da ke ikrarin jihadi.