1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya yi ajalin mutane 24 a Darfur

April 13, 2023

Wani kazamin fada tsakanin kabilun Larabawa da na Massalit da ya barke a Darfur dake Gabashin Sudan ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 24 tare da tilastawa wasu dubbai tserewa daga matsugunensu.

https://p.dw.com/p/4Q1Wv
Janjaweed-Miliz zerstört weiterhin Dörfer in Darfur
Hoto: Scott Nelson/Getty Images

Masu aiko da rahotanni sun ce bayan dauki ba dadi tsakanin kabilun biyu kura ta lafa a birnin bayan isar jami'an tsaro da gwamnatin Sudan ta aike domin kwatar da tarzomar tare kuma da ayyana dokar ta baci a yankin. 

A alkaluman da rundunar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dindin Duniya dake a yankin ta fitar ta ce a yayin tashin hankalin an kone akalla gidaje 50 kurmus kana kuma lamarin ya raba iyalai dubu hudu da matsugunensu.

Da ma dai an cika samun rikicin kabilu a yankin Darfour da ke Gabashin Sudan, kuma idan za a iya tunawa a shekarar 2003 yakin basasa ya barke a yankin wanda ya yi ajalin mutane da yawansu ya kai dubu 300 tare kuma da raba wasu miliyan 2,5 da matsugunensu.