Bangui: Sama da mutane 10 sun halaka
December 26, 2019Wata majiya ta jami'an tsaro ta nunar da cewa mutane 11 zuwa ne 14 suka rasa rayukansu bayan da rikicin ya barke da yammacin ranar Larabar da ta gabata. A nasa bangaren wani limami mai suna Awad Al Karim ya nunar da cewa an kai gawarwaki 16 zuwa masallacin Ali Babolo da ke yankin, yana mai cewa rikicin ya barke ne bayan da 'yan kasuwar yankin PK5 da Musulmi ke da rinjaye suka dauki makamai, domin nuna adawarsu da harajin da tsagerun da ke rike da makaman suka sanya. Wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ke makwabtaka da yankin, ya ruwaito cewa an ji karar harbe-harbe da abubuwa masu fashewa a yammacin Laraba da wayewar garin Alhamis. A jawabinsa, kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar MINUSCA Bili Aminou Alao ya nunar da cewa sun tura dakarunsu zuwa wajen da rikicin ya barke domin dawo da zaman lafiya.