1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimun ƙasashen Bahrain da Yemen na ci gaba da tsananta

March 14, 2011

Zanga-zangar ƙin jinin gwamnati na cin karo da fishin hukumomin da abin ya shafa a ƙasashen Larabawa

https://p.dw.com/p/10Yei
Hoto: AP/youtube

'Yan sandan ƙasar Bahrain sun yi amfani da Borkono mai sa Hawaye wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar ƙin jinin gwamanti a babban birnin Ƙasar wato Manama. Sai dai rahotannin sun nunar da cewa masu adawa da manufofin gwamantin da galibinsu 'yan shi'a ne, sun sha alwashin ci gaba da gudanar da zanga-zangar har sai hakarsu ta cimma ruwa.Tun a jiya Lahadi ne aka fara fiskantar takun saka tsakanin jami'an tsaro da kuma masu bore da suka kafa shingaye domin gurganta zirga-zirga da kuma harkokin saye da sayarwa a Manama. Su dai masu tayar da kayar bayan suna neman gwamnati ta rungumi tsarin raba madafan iko tsakanin sarki da kuma zaɓaɓɓen Firaminista. A ƙasar Yemen ma dai, ana ci gaba da fiskantar fito na fito tsakanin masu kin jinin gwamantin Ali Abdallah Saleh da kuma 'yan sanda da ke neman murkushe boren. Mutane biyu ne dai suka rasa rayukansu a biranen Sana'a da kuma Aden bayan da jami'an tsaro suka yi amfani da karfi domin tarwatsa masu bore da ke nema shugaban nasu ya sauka daga karagar mulki. A Oman kuwa masarautar wannan kasa ta yi alkawarin ware wasu mukamai na gwamanti ga wasu 'yan kasar da ba su da jinin saraunta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita      : Zainab Mohammed Abubakar