Ribar Afirka a taron G7
June 5, 2015
Taron dai na zaman irinsa na farko a bangaren na Buhari da ya dau alkawarin sauyi, ya kuma kama mulkin kasar cikin halin babu. Babu dai kudin gudanar da harkoki na kasar, sannan kuma babu tsaro na al'ummarta a sassa daban-daban, sannan kum babu farashin mai, mai karfi ga sabuwar gwamnatin mai zumudin samar da sauyi.
To sai dai kuma taron na G7 da aka shirya a kasar Jamus, na zaman damar farko ga Buhari da tuni ya samu amincewar turawan bisa bukatu na kasar, domin sake dora ta bisa tafarkin daidai. Ana dai saran yayin taron, shugaban na Najeriya, zai gana da man'yan shugabannnin duniya da suka hada da na Amurka da Jamus a gefen taron, da ke iya samar da kafar dora kasar bisa sabo na ginshiki a rayuwa.
Man'yan matsaloli dai ya zuwa yanzu ga Tarayyar Najeriyar, na zaman hanyar tunkurar karuwar ta'azzarar ayyuka na kungiyar Boko Haram, da kuma sake dawo da dubban miliyoyi na daloli da aka sace aka kai turan domin boyewa.
Batutuwan kuma da a fadar Dr Sadiq Abba, masani kan harkokin siyasa, ke zaman abubuwan da ya kamaci daukar Hankalin na Buhari a yayin tozali da masu fada ajin na Duniya
Duk da cewar dai da kama wuya, ga turawan su kai ga biyan daukacin bukatun kasar ta Najeriya dai, akwai yiwuwar agaji dama hasken jari na waje, wanda kan iya taimakawa Najeriyar sake tsayawa a kafarta, dama cigaba a bugun kirjin giwa a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.
To sai dai kuma ko wane irin tasiri ziyarar ke iya yi ga kokari na gyara ga kasar dai, a tunanin wasu dattawan cikinta dai akwai bukatar taka tsantsan ga Buhari wajen mu'amala da turawan da a baya suka rungumi gwamnatoci, da nufin soyyaya amma kuma suka yi musu wurgi na kadanya bayan raba gari na bukata.
Ko bayan nan dai, sabon shugaban na iya fuskantar kari na matsin lamba na shugabannin, domin hukunta laifukan yakin da ake zargin manyan hafsoshin sojojin kasar da aikatawa yayin yakin a matsayin sharadin samun taimako na makamai dama kila kudi domin tunkarar matsalar.
A baya dai kasar Amurka ta janye tallafin da take baiwa Najeriya a wajen yakin, sakamakon take hakkin jama'a da sojan dake tsakiyar yakin yanzu suke aikatawa. Kuma ko da ranar Juma'a 05.06.2015 Majalisar Dinkin Duniya, ta bi sahu wajen neman tuhumar man'yan kwamandojin yakin. To sai dai kuma ko ma me zai faru, a tunanin Hon Ahmed Babba Kaita, da ke zaman dan majalisar wakilai daga jihar Katsina, babu hujjar dari-dari ga gayyatar shugaba Buhari da ke zaman sabuwa kuma babbar dama ga kasar.
Abun jira a gani dai na zaman sakamakon taron da Buhari zai kasance a cikinsa, har ya zuwa makon gobe. Abin da kuma ke nuna yadda shugabannin kasashen na G7 suka dauki Afirka cikin jadawalinsu.