1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan warware rikicin Ukraine

April 18, 2014

Gwamnatin Ukraine ta ce za ta dauki tsauraran matakai muddin 'yan aware ba su fice daga gine-ginen da suka mamaye ba, inda a hannu guda kuma ta ke shirin yin sulhu.

https://p.dw.com/p/1BktR
Ukraine Demo in Madrid 17.03.2014
Hoto: DW/W. Tscherezki

Gwamnatin ta Ukraine dai ba ta yi karin haske na irin matakan da za ta yi amfani da su ba. Amma kuma ministan harkokin wajen Ukraine din Andriy Deshchytsia ya ce in har 'yan awaren suka kai ga barin wuraren da suke mamaye da su kafin makon na gobe, to gwamnati za ta maida hankali ne kan zaman sulhu wanda kungiyar nan ta tabbatar da tsaro da hadin kan Turai ta OSCE za ta sanya idanu a kai.

Baya ga wannan, gwamnatin ta Ukraine ta ce domin ganin an kai ga faranta wa kowa a kasar da ma kashe wutar rikicin siyasar da ta dabaibaye Ukraine din, Kiev za ta biya bukatun kowa kamar yadda firaministan kasar Arseny Yatsenuik ya shaida. Mr Yatenuik ya ce ''gwamnatin a shirye ta ke ta sasanta da sassan da ke ta da kayar baya: kazalika ta himmatu wajen cika dukannin bukatun al'ummar kasar wanda ba su saba wa doka ba.''

Firaministan Ukraine Arseny Yatsenuik ya ce shirye su ke da su hau teburin sulhu.
Hoto: Reuters

To sai dai duk da wannan, 'yan awaren musamman ma dai na yankin Donetsk wanda Denis Pushilin ke jagoranta sun ce ba za su amince da abinda ya kira romon bakan da Kiev ke yi musu ba har sai su ma sun sauka daga mukamansu.

Pro-russische Kräfte in Donezk Ost-Ukraine Potrait Denis Puschilin
Shugaban 'yan awaren Donetsk Denis Pushilin ya nemi gwamnatin kasar ta yi murabus.Hoto: DW/A.Sawitsky

Su ma dai al'ummomin sauran sassan gabashin kasar da ke tada kayar baya cewa suka yi batun barin wajen da suka mamaye bai taso don kuwa mahukuntan Kiev su ma sun mamaye fadar gwamnatin kasar kuma suna cigaba da mamaye ta har yanzu.

Jama'ar dai sun ce suna son ganin an girka gwamnati ta 'yan ba ruwanmu a Kiev saboda a cewarsu abinda ake da shi yanzu tamkar gwamnatin mulkin soja ce da ta karbe mulki da karfin tuwo kuma ta ke kokarin tursasawa al'umma su yi abinda ta ke so. Wannan yanayi da aka shiga ne ma dai ya sanya kasashen duniya da dama ganin cewar yarjejeniya da aka cimma tsakanin Rasha da Ukraine da Amirka da kungiyar tarayyar Turai ta EU na iya cin karo da matsala duba da irin rashin fahimtar junan da ake cigaba da samu.

Frank Walter-Steinmeier da ke zaman ministan harkokin wajen tarayyar Jamus kuma ya ke daga cikin wanda ke wadanda ke da irin wannan tunani ya ce '' ya zuwa yanzu dai ba za a iya cewa an kai ga cimma matsaya ta zaman lafiya ba. Sai dai a iya cewa an kan godabe na kaiwa ga haka. Ya kyautu 'yan Ukraine su kasance tsintsiya madaurinki daya domin ya kasance nan gaba kasar ta hau turba kyakkyawa ta dimokradiyya da ma dai samun bunkasar tattalin arziki.''

Demonstration von Unterstützern der ukrainischen Regierung in Donezk
Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter-Steinmeier ya nemi mutanen Ukraine su daidaita don cigaban kasar.Hoto: GMF

Wannan yanayi da ake ciki dai ya sanya da dama ganin cewar zaben shugaban kasar ta Ukarain da ke tafe cikin watan gobe ka iya cin karo da tsaiko duba da irin yadda wutar rikici ke cigaba da ruruwa. Wani abu kuma da ake cigaba da nuna damuwa a kai shi ne batu na mutunta hakkin bani adama da na 'yanci fadin albarkacin baki a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe