1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Trump da Kim tana kasa tana dabo

Abdul-raheem Hassan LMJ
May 28, 2018

Har yanzu dai ana cikin hali na rashin tabbas dangane da tattaunawa tsakanin shugaban Amirka Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

https://p.dw.com/p/2ySp5
USA Nordkorea - Donald Trump und Kim Jong Un - TV
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Jin-man

Bayan shan suka kan matakin da shugaban Amirka Donald Trump ke fuskanta bayan soke ganawa tare da takwarsansa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un da aka tsara a ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa, a yanzu haka Trump din na shirin lashe amansa inda ya tura tawaga zuwa Koriya ta Arewan domin sake shirin tattaunawar kamar yadda aka tsara a kasar Singapore. A nata bangaren Japan na bayyana tasirin cimma ganawar wajen warware takaddama da ke tsakanin kasashen Koriya da Japan din. Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya ce ganawarsa da Shugaba Trump ta ba shi tabbacin za a kai ga cimma ganawa tsakanin Shugaba Kim da Trump.

Nordkorea Zerstörung Atomtestgelände in Punggye-ri
Koriya ta Arewa ta lalata tashar gwajin nukiliyartaHoto: Reuters/News1

Koriya ta Arewa ta yi abin a yaba mata

Masu nazarin al'amuran siyasan na ganin a wannan gaba Koriya ta Arewa ta taka rawar gani na nuna bukatar warware tsamin dangantar da ke tsakaninta da Amirka. John Delury farfesa ne a ke nazari kan yankin Asiya a jami'ar Yonsei ya kuma ce ''Koriya ta Arewa ta nuna halin kwarai cikin watanni shidan da suka gabata ba tare da gwajin makamin nukiliya ba, ta saki Amirkawa uku da ta ke tsare da su. Sannan ta rusa cibiyar gwajin makamanta. A dangane da haka muna ganin shugabannin na da damar cimma wannan fata."

A makon jiya ne dai Shugaba Trump ya sanar da soke ganawarsa da Kim a kasar Singapore, sa'o'i kalalilan bayan da Koriya ta Arewa ta rushe cibiyar gwajin makamanta na Nukliya. Yanzu dai ranar 12 ga watan Yuni ne za ta tabbatar da cika alkawarin Shugaba Trump.