1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin aiki ga matasa na haifar da fargaba a Najeriya

December 26, 2017

Kungiyoyin farar hula a Najeriya sun nuna fargaba game da halin da kasar za ta fada ciki sakamakon karuwar rashin aikin yi ga matasa.

https://p.dw.com/p/2pxvO
Symbolbild Gewalt in Nigeria
Rashin aikin yi na daga cikin dalilan yawan samun hargitsin matasa a arewacin NajeriyaHoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

Kungiyoyin suka ce rashin aiki na yin barazana ga yanayin zamantakewa da zaman lafiyar al’ummar kasa. A saboda haka suka bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su hanzarta daukar matakai domin shawo kan matsalar ta hanyar inganta yanayi da bullo da hanyoyin tallafa wa matasa ayyukan yi don samun dogaro da kai a cewar Dr Auwal Aliyu Abubakar shugaban kungiyoyin fararen hula a Kaduna.

“Idan matashi yana da san’ar yi, ba shi da lokacin da zai shiga harkar shaye-shaye ko sara suka ko kuma sace-sace. A saboda haka wannan matsala ce wadda ta fuskanci kowa kuma take damun kowa.”

Nigeria Studenten in Jos
Dalibai na kwalejin horon fasaha a Jos NajeriyaHoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall

A kowace shekara ana yaye dubban dalibai a jami’o'i da kwalejojin kimiyya da fasaha da makarantun horar ungozoma wadanda a karshe ke komawa zaman kashe wando saboda rashin aikin yi, lamarin da ke jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa.

Kwamarade Abubakar Abdullahi jigo ne a kungiyar manema aikin yin a arewacin Najeriya. Ya baiyana irin wahalhalun da matasan da suka kammala karatu musamman na jami’a suke ciki sakamakon karancin aikin yi.

“Mutane da dama sun gama makaranta babu aiki, wadanda suka yi sa’ar samun aikin kuma albashin ba isa yake yi ba."

Sai dai a nata bangaren gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana bakin kokari na samar wa matasan aiki a cewar mai magana da yawun gwamnatin Hon Sa’idu Adamu.

Nigeria Bombenanschlag
Taron jama'a a jihar Kadunan Najeriya bayan tashin wani bam a shekarun bayaHoto: AP

Kungiyoyin farar hular dai sun ba da shawarar gwamnati ta dauki matakan daidaita rayuwar matasa ta hanyar hana shigar da miyagun kwayoyi cikin kasar wanda ke kassara rayuwar matasa.

Bugu da kari sun yi kira ga gwamnatin ta bude cibiyoyin da matasa za su koyi sana’oi tare da tallafa musu yadda za su rike kansu bayan sun kammala horon sana’ar.

Masana harkar tsaro dai sun baiyana cewa matsalar rashin aikin yi ita ce ta haifar da karuwar matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan ayyuka da matasa ke aikatawa.