Rasha za ta sasanta Amirka da Koriya ta Arewa
December 26, 2017Talla
Gwamnatin kasar Rasha ta sanar cewa tana yunkurin sulhunta tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen Amirka da Koriya ta Arewa, in har bangarorin biyu sun amince da wannan tayin.
Ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya yi kira ga kasashen biyu da su hau teburin sulhu bayan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kakaba wa kasar ta Koriya ta Arewa takunkumi a makon da ya gabata, sakamakon gwajin makaman kare dangi da kasar ke ci gaba da yi wanda ke zama barazana ga duniya baki daya.