Putin zai rage luguden wuta a Ukraine
March 29, 2022Talla
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta ce an kammala tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da kungiyoyin sasantawa na Ukraine da aka gudanar a birnin Santanbul.
Gwamnatin Rasha ta yanke shawarar katse ayyukan dakarunta a kusa da biranen Kyiv da Chernihiv na Ukraine, mataimakin ministan tsaron Moscow Alexander Fomin ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan tattaunawar hukumomin kasashen biyu da sukaa yi a birnin Santanbul na kasar Turkiyya don kawo karshen rikicin.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce kimanin mutane miliyan 18 ne a Ukraine za su bukaci agajin gaggawa sakamakon barnar da sojojin Rasha suka haddasa.