1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta bude tashar makamashin gas a Turkiyya

October 13, 2022

A wata ganawa ta keke da keke tsakaninshi da Shugaba Recep Tayyip Erdogan, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce Moscow na duba yiwuwar bude tashar makamashin iskar gas a Turkiyya.

https://p.dw.com/p/4I8xV
Hoto: Sputnik/Vyacheslav Prokofyev/Pool via REUTERS

Mahukuntan na Moscow dai na ganin a halin da ake ciki Turkiyya ita ce kasar da za su fi aminta da ita wajen fitar da makamashinsu zuwa kasashen waje, bayan takunkuman da kasashen yamma suka kakaba musu.

Wannan dai shi ne karo na 4 da shugabannin ke haduwa a tsukin watanni 3 wanda ya kai ga kasashen Turai na kira ga Shugaba Erdogan da ya mutunta matsayarsu ta ladabtar da Rasha bisa mamayar da take ci gaba da yi a Ukraine.

Turkiyya a nata bangaren na kokarin shiga tsakanin kasashen yamma da Rasha don magance tsamin dangantakar da ke ci gaba da lalacewa a tsakaninsu.