1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Za a rantsar da Putin wa'adi na hudu

Abdul-raheem Hassan MNA
May 7, 2018

'Yan sanda a Rasha sun saki madugun adawa da sauran daruruwan masu zanga-zanga da aka tsare kwana guda kamin rantsar da shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/2xH0d
Russland Präsident Putin
Hoto: picture-alliance/TASS/M. Klimentyev

Hukumomin kasar Rasha sun saki jagoran adawa Alexei Navalny tare da mukarrabansa 1,500 da aka tsare yayin wani gangamin adawa da shugaba Vladimir Putin a karshen mako. 'Yan sanda sun zargi Navalny da shirya gangami ba tare da umarnin hukumomi ba. Wannan dai ba shi ne karon farko da madugun adawar ke karambatta da 'yan sanda kan hada kan 'yan kasar don nuna adawa da gwamnati ba.

Kungiyar Tarayyar Turai EU da sauran hukumomin kasa da kasa na Allah wadai kan yadda 'yan sanda ke amfani da tsinin bindiga kan 'yan adawa yayin tarwatsa duk wata zanga-zangar adawa da gwamnati a fadin kasar Rasha.

Shugaba Vladimir Putin zai sha rantsuwar ci gaba da mulkin kasar Rasha wa'adi na hudu a dai-dai lokacin da yake fuskantar suka daga kasashen duniya kan mamaye yankin Kirimiya. 'Yan adawa a kasar kuma na kalubalantar shugancin sa da gurgunta tattalin arzikin Rasha.