Rasha ta yi watsi da tayin Amurka
January 18, 2024Lavrov ya ce hakan ba zai yiwu ba muddin Amurka da kawayenta na ci gaba da goya wa Ukraine baya da ma ba ta makamai a yakin da suke yi.
Da yake jawabi a taronsu na shekara-shekara, Lavrov ya zargi kasashen yamma da rura wutar rikici a duniya da ma ingiza Ukraine.
Babban jami'in diplomasiyyar Rashar, ya ce akwai bukatar Amurka ta sauka daga matakin da ta hau a kan kasarsa idan har tana neman wani sulhu da su.
A cewarsa Rasha ba ta yi wa kasashen yamma barazana da makamin na nukiliya ba, ya kuma gargadi kasashen Amurka da kawayenta da kada su kuskura su yi musu wannan barazanar.
Dangantaka tsakanin Rasha da kasashen yamma dai ta jima da yin tsami tun bayan da ta kaddamar da mamaya a kan Ukraine a Fabrairun shekarar 2022.
Karin bayani: Cacar-baka ta barke a tsakanin Rasha da kasashen yamma