Rasha ta janye daga wakilci a NATO
October 18, 2021Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa za ta dakatar da aiki na wakilci a kungiyar tsaro ta NATO/OTAN da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam daga farkon wata mai zuwa na Nuwamba sakamakon kwace takardun aiki na jami'an diflomasiyar kasar. Bugu da kari, Rasha za ta rufe ofishin NATo da ke birnin Moscow fadar gwamnatin kasar.
Sergei Lavrov ministan harkokin wajen na Rasha ya fadi haka yayin taron manema labarai, inda ya ce haka na zama martani kan karbe takardun aikin jami'an diflomasiyan Rasha guda takwas daga kungiyar tsaron ta NATO bisa zarge cewa 'yan leken asiri ne da ake rufa-rufa.
Sai dai a cikin martani Heiko Maas ministan harkokin wajen Jamus ya bayyana matakin na Rasha a matsayin abin takaici. Maas ya shaida wa manema labarai a Luxembourg cewa kasashen kungiyar tsaron ta NATO suna shirye da tattaunawa da mahukuntan Rasha maimakon fito na fito.