1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta bukaci nadamar Birtaniya

Salissou Boukari
March 19, 2018

Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta bakin mai magana da yawunta Dmitri Peskov, ta nemi kasar Britaniya da ta gabatar mata da cikakar shaidar kan mumunan zargin da take yi mata, ko kuma ta nemi gafararta.

https://p.dw.com/p/2uZxd
Der Sprecher des russischen Präsidenten Dmitri Peskow
Dmitri Peskov mai magana da yawun fadar shugaban kasar Rasha ta KremlinHoto: picture-alliance/M.Metzel

Kwana guda bayan zaben shugaban kasar da ya bai wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha nasara da gagarumin rinjaye na kashi 76.7 cikin 100, fadar shugaban na Rasha ta Kremlin ta bakin mai magana da yawunta Dmitri Peskov, ta nemi da kasar Britaniya ta gabatar mata da cikakkiyar shaida kan zargin da take yi mata na hallaka tsohon dan leken asirin kasar ta Rasha da ke zaune a Britaniya, ko kuma Britaniyar ta nemi gafarar Rasha kan wannan zargi.

Peskov ya ce ko ba jima ko ba dade, dole ne sai Britaniya ta bai wa Rasha amsa kan wannan mugun zargi da ta yi mata wanda ta ce marar tushe ne, inda ya danganta zargin da Britaniya ta yi a matsayin wasu tarin karairayi da cin mutunci ga Rasha, wanda ma ba a san ma'anarsu ta yin hakan ba.

Kasar ta Britaniya dai ta zargi Rasha da hannu wajen yunkurin kisan tsohon jami'in leken asirin kasar Rasha da ke zaune a Britaniya, ta hanyar saka masa guba tare da 'yarsa, wanda hakan ya haifar da babbar tankiya ta diflomasiyya tare da korar jami'an diflomasiyya na kasashen biyu.