1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamnoni a yankunan kasar Rasha

Emily Sherwin MNA/LMJ
September 11, 2020

A ranar Lahadi ake gudanar da zabukan yankuna a kasar Rasha domin zabar sababbin gwamnoni da wakilan majalisun kananan hukumomi. Masharhanta na ganin zaben a matsayin zakaran gwajin dafi na irin yanayin da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/3iMCE
Berlin Nawalny in Charite | Spezialtrage
Alexei Navalny na karbar magani a JamusHoto: Getty Images/M. Hitij

Jagoran 'yan adawa, Alexei Navalny da yanzu haka ake masa magani a wani asibiti da ke Jamus bisa wata guba da aka sanya masa, ya yi ta yin gangamin ganin an karya lagon jam'iyyar da ke jan ragamar mulki a Rashan. A shekara mai zuwa ne dai za a yi zaben 'yan majalisun dokokin kasar ta Rasha.

Karin Bayani: Navalny ya fara farfadowa

Magoya bayan Alexei Navalny da ke zama babban mai adawa da gwamnatin shugaban Rashan Vladimir Putin na ganin jagoransu, a matsayin wata babbar barazana ga fadar mulki ta Kremlin. Wannan dalilin ne ma  a ganinsu ya sanya aka saka masa guba. Navalny yana birnin Novosibirsk na yankin Saberiya, kafin a saka masa gubar da ya sa a dole aka garzayo da shi nan Jamus da yi masa magani.

Karin Bayani: Rasha da Jamus na sa-in-sa kan Navalny

Sergei Boiko dan siyasa kuma dan takarar neman kujerar majalisar yanki na amfani da kafar sada zumunta ta internet, wajen tattaunawa da masu zabe a birnin Novosibirski. Ya yi alkawarin kakkabe yankin Saberiya da abin da ya kira 'yan siyasa masu cin hanci da rashawa. Shi ne dai shugaban kawancen 'yan takara 31 daga bangaren adawa da suka lashi takobin kifar da jam'iyyar da ke mulki ta United Russia.

Russland Nowosibirsk | Wahlkampagne | Sergei Boiko
Sergei Boiko dan takarar kujerar majalisar yankin NovosibirskHoto: DW/E. Sherwin

Boiko ya hada karfi da jagoran 'yan adawa Alexei Navalny da a cikin wani faifayen bidiyo ya nuna yadda matsalar cin hanci da rashawa ta yi katutu tsakanin 'yan siyasar jam'iyyar ta United Russia da ke yankin. Sai dai jim kadan bayan nadar bidiyon aka saka masa guba. Ya yi kira da a kada wa 'yan takarar da ke da manufar kifar da jam'iyyar da ke mulki kuri'a.

Karin Bayani: Rasha: Matakan ba sani ba sabo kan 'yan adawa

Birnin Novosibirsk dai shi ne babban birnin yankin Sabiriya, yana kuma da yawan al'umma milyian daya da rabi. Sai dai jam'iyyar da ke mulki ta ce za ta ci gaba da rike rinjayen da take da shi a yankin, a cewar Mamwel Agajan 'yar jam'iyar ta United Russia. Sai dai wasu na da ra'ayin cewa ba kowa ne ya gani a kasa ba a birnin. 'Yan adawa irinsu Sergei Boikom sun ce za su sama wa birnin na Novosibirski sabuwar alkibla, idan kawancensa ya samu rinjaye. Sai dai kalubalensa shi ne, yadda zai gamsar da jama'a cewa kuri'unsu za su iya kawo sauyin da ake bukata a Rasha baki daya.