Nijar ta kulla yarjejeniyar tsaro da Rasha
January 17, 2024Gwamnatin Rasha ta cimma yarjejeniyar kara karfafa huldarta ta fannin tsaro da Jamhuriyar Nijar, hukumomin Moscow, sun ce a yayin wata ganawarsu da firaministan rikon kwaryar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine da mukarabansa, sun kulla yarjejeniyar tsaro da kara inganta hulda ta fannonin ci gaba da dama a tsakanin kasashen biyu.
Karin Bayani : Nijar: Sabon babin hulda da manyan kasashe
Tun da jimawa Moscow ke fatan fadada komarta a wasu yankunan yammacin Afirka, ciki har da Jamhuriyar Nijar da sojoji suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya a cikin watan Yulin 2023, tare da daukar matakan korar dakarun Faransa daga kasar a karshen shekarar 2023, matakin da ya kai jami'an gwamnatin Rasha ziyara a Nijar a cikin watan Dismaban 2023.
Karin Bayani : Nijar: Ziyarar jami'an gwamnatin Rasha
Tawagar ta Jamhuriyar Nijar da ke rangadin za ta ci gaba zuwa wasu kasashe, ciki har da Turkiya da Iran, bayan da ta yada zango a birnin Moscow.