SiyasaAfirka
EU : Corona da Rasha na kan gaba a taron koli
December 16, 2021Talla
Batun rashin cikakken tsari don tunkarar sabon nau'in annobar corona na "Omicron" da na jibge sojojin Rasha a iyakarta da Ukraine na kan gaba daga cikin muhimman btutuwan da hukumomin kasashen EU za su mayar da hankali akai.
Babban jami'in dioflomasiyar kungiyar Josep Borrell, ya bayyana cewa kasashen kungiyar EU na goyon bayan Ukraine kan rikicinta da gwamnatin Moscow, kana kuma duk wasu matakan da Rasha ke dauka da suka saba ka'ida ka iya fuksntar hukunci mai tsanani daga kasashen.
Ana sa ran shuwagabannin su kebe waje daya don cikakken nazari kan wasu jerin takunkuman da suke ganin ya dace su kakaba wa Rasha a gabanin fitowa fili su bayyana su.