1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana zagin shugabanni a Rasha

Yusuf Bala Nayaya
March 18, 2019

Putin ya rattaba hannu kan dokar duk da suka daga kungiyoyi na kare hakkin bil Adama wadanda ke cewa wannan doka za ta iya bude kofa wajen yin nakasu ga 'yanci na fadin albarkacin baki.

https://p.dw.com/p/3FGuH
ZDF-Doku Putin und die Mafia
Hoto: ZDF/David Lemarchand

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha a wannan rana ta Litinin ya rattaba hannu kan wata doka me cike da cece-ku-ce wacce za ta ba wa kotu damar cin tara ko kuma tsare mutumin da aka kama da laifi na nuna rashin da'a ga mahukunta ko ma taka burki ga kafafan yada labarai da ake ganin "labaran karya" ne.

Putin ya rattaba hannu kan dokar duk da suka daga kungiyoyi na kare hakkin bil Adama wadanda ke cewa wannan doka za ta iya bude kofa wajen yin nakasu ga 'yanci na fadin albarkacin baki.

Karkashin wannan doka dai wanda aka kama da laifin kin mutunta mahukunta a karo dabam-dabam zai iya share tsawon kwanaki 15 a tsare ko kuma ya fuskanci tara. Kafar yada labarai da aka samu da labarai na karya ana iya rufewa ko rufe shafinta na intanet. Wanda kuwa suka ba da labarai da ya haifar da tashin hankali ko ma dalili na kisa ana iya cinsu tarar sama da Dala dubu 22.