Ranar yaki da kaciyar mata a duniya
February 6, 2020A cewa Majalisar Dinkin Duniya akwai kimanin ‘yan mata miliyan 4 da dubu dari da yanzu ke fuskantar barazanar yi musu kaciya a fadin duniya a cikin wannan shekara da muke ciki.Najeriya ce ta uku tsakanin kasashen duniya da aka fi samun al’adar yi wa mata Kaciya, inda alkaluman majalisar ya nuna cewa kashi ashirin da biyar ko kuma ‘yan Mata da manyan mata miliyan goma sha tara da dubu dari tara ne tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa arba'in da tara aka yi wa kaciya tsakanin shekara ta 2004 zuwa shekara ta 2015.
Wannan a cewar Majalisar Dinkin Duniya abu mai tada hankali da ya kamata a tashi tsaye a magance domin ceto ‘yan matan da wannan cin zarafi da ake musu wanda ake alakantawa da al’ada ko kuma ma addini.
Har yanzu a wasu sassan Najeriya kamar Arewa maso Gabashi da ake samun wasu kabilu na yi wa mata kaciya duk da fadakarwar da ake yi dama yadda hukumomi suka tashi tsaye a yaki da al’adar. Akwai dai wasu iyaye da su yi imanin cewa tun da addini bai hana ba su kam za su ci gaba da yi inda kuma akwai wadanda basa yi ba wai don ba kyau ba, sai dai don basu da ra’ayin yi kuma ba'a yi a tsarin al’adun su.
Masana da masharhanta na ganin sai dole gwamnatoci sun tashi tsaye wajen ilmantar da al’umma watakila da kuma samar da dokoki da za su zama barazana ga masu yin wannan al’ada.