1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ranar girmama wadanda ta'addanci ya shafa a duniya.

Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2023

Ranar 21 ga watan Agusta, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin girmama wadanda ta'addanci ya shafa a duniya.

https://p.dw.com/p/4VPls
Wasu 'yan gudun hijira a jihar Borno
Wasu 'yan gudun hijira a jihar Borno Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu mutuwar kusan mutane 23,000 tsakanin 2007 da 2022 a yankin Sahel da aka fi fuskantar hare-haren ta'addanci a 'yan shekarun nan. Sai dai cibiyoyi daban daban na tallafa wa wadanda ta'addancin ya raunata.

Maloum Abba yana zaune da iyalinsa a Ngouboua da ke yankin tafkin Chadi. Hasali ma shekaru hudu da suka gabata ne 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wa kauyensu hari. Sai da ya tsere da wasu daga cikin iyalansa don samun mafaka a kusa da Bol da ke zama babban birnin lardin tafkin Chadi. Sai dai ya yi matukar kaduwa saboda ta'addacin ya raba shi da sana'arsa ta kamun kifi

Najeriya| Wasu 'yan gudun hijira a Pulko
Najeriya| Wasu 'yan gudun hijira a PulkoHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

"Lokacin da ‘yan Boko Haram suka zo kauyenmu kusan shekaru hudu da suka wuce, sun kashe ‘yan uwanmu, sun kuma kona gidajenmu, sun kwashe mana kayanmu. Sun yi garkuwa da 'ya'yanmu da matanmu. Mun rasa komai namu. Yanzu ba zan iya kamun kifi ko noma ba. Matanmu ba sa iya sayar da kifi kamar yadda suka saba, yanayin rayuwarmu yana da matukar wahala. Muna matukar tsoro".

Karin bayani: Nijar: Mutane sun tere saboda ta'addanci

Duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tallafa wa wadanda matsalar ta'addanci ta shafa da wadanda suka tsira daga ta'addanci, amma dai wannan kalubale na tsaro na ci gaba da yaduwa a yankin Sahel. Kuma wadanda matsalar tsaro ta shafa na rayuwa cikin mawuyacin hali, walau a tarayyar Najeriya ne da ke fama da 'yan ta'addan Boko Haram, zuwa Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso da ta fada tarkon 'yan bindiga a baya-bayan nan.

Nigeria I Daruruwan 'yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram
Nigeria I Daruruwan 'yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko HaramHoto: Getty Images/AFP/Stringer

A cikin shekarar 2021 ga misali, Zirbrine Abassa Seyni ya shaidar da yadda aka kashe mahaifinsa a wani harin da masu ikirarin jihadi suka kai a yankin Tillabéri da ke kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar. Shi dai Zirbrine Abassa Seyni ya yi Allah wadai da rashin daukar matakan da suka dace daga bangaren gwamnati domin yaki da ta'addanci a wasu jihohin Nijar.

"An kashe mahaifina a wannan harin tare da wasu ‘yan uwana 17 a masallacin kauyenmu a tsakiyar sallar isha'i. A yau, bayan rasuwar mahaifina a wannan harin, babu abin da zai iya maye gurbinsa. Ya bar mu da matansa da marayu".

A tsakanin shekarar 2007 zuwa 2022, a yankin Sahel kadai, an samu hare-haren masu ikirarin jihadi kusan 7,000. Wadannan hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 23,000, a cewar rahoton 2023 na cibiyar Global Terrorism Index, wata cibiyar tattalin arziki da zaman Lafiya. Rahoton ya ce a cikin shekaru 15 da suka gabata, hare-haren ta'addanci a yankin Sahel sun karu da kusan kashi 2,000%. Sai dai kasashen yankin Sahel har ma da kungiyar tsaro ta G5 Sahel, wadanda suke fuskantar raunin na karfin soja, sun gaza nasarar tunkarar kungiyoyin da ke dauke da makamai.