1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ramadan: An nemi 'yan kasuwa su sassauta farashi

May 27, 2017

Kungiyar mata masu da'awa a Najeriya tare da limaman coci-coci a kasar sun bukaci 'yan kasuwa da su sassauta farashin kayayyakin masarufi da ake yin amfani da su a lokacin buda baki na azumin watan Ramadana.

https://p.dw.com/p/2de3O
Nigeria Abuja Markt in Gwarinpa
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

Wata Tawagar limaman coci-coci ta kaddamar da wani kampe irin sa na farko a cikin kasuwannin jahar kaduna a kan bukatar tattaunawa da dukkanin shugabannin ‘yan kasuwa kan rage farashin kayayyakin abinci da musulmai masu azumi ke amfani da su wajan bude baki. Tawagar da ke karkashin jagorancin Pastor Yohanna Buru ta ce ta shiga kasuwannin ne domin janyo hankalin ‘yan kasuwar a kan mahimancin karya farashin dukkanin abubuwan da suke sayawa a wannan lokacin domin rabauta da lada a cikin watan na azumi mai alfarma.

Nigeria Tomaten auf dem Markt in Port Harcourt
Kayan masarufi kan yi tashin gwauron zabi a lokutan azumi, batun da jama'a kan koka da shiHoto: DW/M. Bello

Kasuwannin da damar gaske ne dai a cikin kananan hukumomi 23 da ke a fadin jahar ta Kaduna limaman cocin suka kai ziyara domin janyo hankalin ‘yan kasuwar da nufin ganin sun kai ga cimma nasarar da suka sanya a gaba ta ganin musulmi sun samu sukunin yin azumi cikin sauki ba tare da fuskantar wani kalubale ba. Baya ga wannan kira da limaman cocin suka yi, su ma mata masu da'awa a jihar ta Kaduna sun yi makamancin wannan kira inda suka nemi 'yan kasuwa da su sassauta farashi domin musulmi su samu sauki na sayen kayan masarufi. Har wa yau wadannan kungiyoyi biyu sun kuma bukaci gwamnati da attajirai da su taimakawa wanda ba su da galihu don su samu damar yin azumi cikin yanayi mai kyau.